Harin 'yan bindga ya kashe sojojin Burkina Faso 50
July 30, 2025Talla
Ana zargin kungiyar Jama'at Nasr al-Islam wal-Muslimin ko JNIM da kai harin a ranar Litinin da ta gabata a sansanin Dargo da ke lardin Boulsa a yankin arewacin kasar ta Afirka ta Yamma.
Majiyoyin biyu, wadanda suka yi magana da kamfanin dillancin labarai na Associated Press bisa sharadin ba za a bayyana sunansu ba, saboda suna fargabar sojoji, sun ce 'yan bindiga kusan 100 ne suka kai harin, kuma sun kone tare da dibar ganima a sansanin bayan kashe-kashen.
Har yanzu gwamnatin sojan kasar ta Burkina Faso ba ta fito fili da tabbatar da harin ba.