Harin 'yan bindiga ya halaka mutane a Katsina da ke Najeriya
August 19, 2025Rahotanni daga Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane 13 sanadiyyar harin 'yan bindiga a jihar Katsina da ke arewacin kasar, duk kuwa da sulhun da wasu yankuna suka yi da 'yan bindigar da suka addabe su, kamar yadda wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nunar.
Harin ya faru ne a unguwar Mantau ta karamar hukumar Malumfashi a wannan Talata, bayan da 'yan bindigar suka far wa wani masallaci.
Karin bayani:Mutane 25 aka ceto a Najeriya bayan kifewar jirgi a Sokoto
Ko da yake karamar ta Malumfashi da harin ya shafa ba ta cikin wadanda suka cimma irin wannan yarjejeniyar sulhu da 'yan bindiga.
Wadannan munanan hare-haren 'yan bindiga sun fi kamari a jihohin arewa maso yammacin Najeriya, inda suke sace shanun jama'a da garkuwa da mutane da kuma sanya wa manoma haraji, ko da yake gwamnatin kasar na cewa tana iya kokarinta na magane matsalar tsaron.