Harin ta'addanci ya halaka mutane 44 a Jamhuriyar Nijar
March 22, 2025Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku, sakamakon kisan fararen hula 44 da 'yan ta'addar kungiyar IS suka yi a yankin kudu maso yammacin kasar, tare da jikkata wasu 13.
Karin bayani:'Yan bindiga sun halaka mutane kusan 20 a Jamhuriyar Nijar
Sanarwar da ma'aikatar cikin gida ta kasar ta fitar ta gidan talabijin na kasar, ta ce harin na ranar Juma'a ya faru a masallacin Fambita na kauyen Kokorou, bayan 'yan bindigar sun yi wa masallatan kawanya dauke da makamai, sannan suka bude musu wuta.
Karin bayani:Harin ta'addanci ya halaka mutane 39 a Jamhuriyar Nijar
Haka zalika maharan sun kona gidajen jama'a da kuma kasuwar garin, da ke dab da iyakar Nijar da Burkina Faso da kuma Mali, inda gwamnatin kasar ta sha alwshin zakulo maharan don hukunta su daidai da abin da suka aikata.