Harin ta'addanci na karuwa a Jihar Filato
April 15, 2025Ana zaman dar- dar tsakanin al'ummomi da ke kauyukan gundumar Kwall cikin karamar hukumar Bassa, bayan sabon harin 'yan bindiga, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane da dama tare da raunata wasu.
Mazauna yankin sun bayyana mawuyacin halin da suke ciki bayan harin yan bindigar. Mr Samuel Jugu, shine jami'in hulda da jama'a na kungiyar raya cigaban al'ummar Irigwe ta kasa, yace bayan wadanda suka rasu, akwai mutane da dama da suka sami raunuka suna kwance a asibitoci daban daban suna karban magani
Wannan sabon hari na yan bindiga na zuwa ne kwanaki kalilan bayan wanda aka yi a karamar hukumar Bokkos, inda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da kona dukiyoyi, don haka wasu ke cewar akwai sakacin gwamnatin Filato dangane da matakan dakile wadan nan hare hare, kasancewar gwamnan Filato Calen Mutfwang, ba ya zuwa wuraren hare haren ke faruwa don ganewa idon sa da nufin daukar matakai na zahiri.
Wasu suna danganta rikicin da manoma da makiyaya yayin da wasu ke cewa rikici ne na kabilanci ke sanadin rasa rayukan al'umma.