Harin ta'addanci a jihar Bornon Najeriya ya halaka mutane
June 2, 2025Harin ta'addanci a jihar Bornon Najeriya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 9, bayan tarwatsewar bam a tashar kauyen Mairari da ke Guzamala, kamar yadda 'dan majalisar jiha mai wakiltar yankin Abdulkarim Lawan ya tabbatar.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito Abdulkarim Lawan wanda shi ne shugaban majalisar dokokin jihar Borno na cewa tuntuni mutanen kauyen suka tsere daga muhallansu, sanadiyyar yawaitar hare-haren ta'addanci da suka addabe su.
Rundunar 'yan sandan kasar ta bakin mai magana da yawunta a Borno Nahum Kenneth Daso ta tabbatar da cewa lamarin ya faru a ranar Asabar, to amma har zuwa wannan lokaci tana kan tattara bayanai a kai.
A wani labarin 'yan bindiga sun kashe mutane 25 a jihar Benue ta tsakiyar Najeriya a hare-hare guda biyu ranar Lahadi, wanda ya samo asali daga rikicin makiyaya da manoma a yankin, kamar yadda rundunar 'yan sandan kasar ta tabbatar.
Ita ko kungiyar ta'addanci ta JNIM mai alaka da Al Qaeda ta dauki alhakin mutuwar sojojin kasar Mali sama da 30 ranar Lahadi, bayan kwace iko da sansaninsu na Boulkessi da ke tsakiyar Mali, kusa da iyakarta da Burkina Faso.
Kimanin sojoji sama da 400 'yan bindiga suka halaka a kasashen Mali Jamhuriyar Nijar da kuma Burkina Faso daga farkon watan Mayun jiya zuwa karshensa.
Wasu fayafayan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna yadda 'yan ta'addan ke murkushe sojojin a sansanoninsu, ko da yake kamfanin dillancin labarai na Reuters bai tabbatar da sahihancinsu ba.
Kasashen Mali Nijar da kuma Burkina Faso sun jima cikin yanayin hare-haren ta'addanci, wanda janyo juyin mulkin sojoji da suka alkawarta kawo karshen matsalar tsaron ,amma har yanzu bata sauya zani ba.
Ko a wannan Litinin wata majiyar soji ta tabbatarwa kamfanin dillancin Faransa AFP cewa 'yan ta'adda sun far wa sansanin sojin birnin Timbuktu na Mali, inda suka fafata da sojojin kasar.