SiyasaTurai
Harin jirgi marar matuki na Ukraine ya kashe mutane a Rasha
August 11, 2025Talla
Harin jirgi marar matuki da Ukraine ta kai Rasha ya halaka mutane 3, yayin da wasu 4 suka jikkata, a garuruwan Tula da Nizhny Novgorod, bayan da hare-haren suka nufi Moscow babban birnin kasar.
Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce dakarunta sun samu nasarar kakkabo jirage 59 marasa matuka da Ukraine ta harba mata cikin dare.
Karin bayani:Trump zai gana da Putin a Amurka
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito kasashen biyu na ikirarin kaucewa kai hare-hare kan fararen hula, a yakin na tsawon sama da shekaru 3, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban jama'a.