Harin Isra'ila ya halaka daruruwan mutane a Gaza
March 18, 2025Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce shi ya bayar da umurnin luguden wutar bayan tuntubar fadar White House ta Amurka.
Wannan harin na bazata ga al'ummar Falasdinawa ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane 400 ciki har da mata da yara kananan da kuma tsofaffi a cewar kamfanin dillancin labarai na Associated Press.
Harin da wasu al'ummar suka ce na ban mamaki ne ya zo ne ana tsakiya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tun watan Janairu albarkacin sa baki da kasashen Qatar da Masar da kuma Amurka suka yi.
Ko da ya ke wasu sun yi zaton faruwar irin wannan farmakin tun bayan da Isra'ila ta toshe shigar da kayan agaji zirin mai mutane a dankare da ke bukatar agajin abinci da magunguna da dai sauransu musamman a wannan watan na Ramadan.
Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya ce ya bayar da umurnin luguden wutan ne saboda rashin ci gaba da ake samu a tattaunawar tsawaita tsagaita wuta, Ko da yake wasu na ganin shi ya yi ta jan kafa wajen shiga zagaye na biyu na tsagaita wutar.
Hukumomi suka ce yanzu aka fara a jerin hare-haren da Isra'ilar ke kaiwa kuma sai ta tabbatar an sako duka mutanenta da ke hannun Hamas.
Jakadan Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya Danny Danon ya ce Isra'ila ta dukufa ne wajen ganin an sako mutanenta da ke hannu.
"Ya ce sojojin saman Isra'ila sun fara kaddamar da hare-hare kan Hamas a Gaza. Za mu nuna babu tausayi ga makiyanmu. Bari in bayyana muku baro-baro, Isra'ila ba za ta tsaya ba har sai duk mutanenmu sun dawo gida. Muna so mu sanar wa Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya cewa idan suna son kawo karshen yakin Gaza to dole su tabbatar mutanenmu sun dawo. Mun dukufa wajen ganin dawo da su gida."
Fadar White House ta Amurka dai ta ce Isra'ila ta tuntube ta kafin far wa zirin na Gaza a sabbin hare-haren, kuma gwamnatin ta Amurkan ta ce ta goyi bayan matakin domin idan aka tafi a haka, Isra'ila za ta yi nasara.
Da yake magana kan yadda hare-haren suka shafi mutane Daraktan asibitocin Gaza Mohammed Zaqout ya ce Isra'ilar ta halaka mutane a wurare daban-daban na kasar.
A yau, masu mamaya sun kashe mutane a sassa daban-daban na Gaza kuma sama da mutum 400 sun rasa rayukansu sannan daruruwa sun zo asibiti da raunuka masu muni ciki har da karaya da kuna suna bukatar jinya ta gaggawa. A dukkan wurare aka yi wadannan kashe-kashe.
A martaninta kan sabbin hare-haren na Talata da suka haddasa mummunan asarar rayuka, kungiyar Hamas ta ce Isra'ilar ta sadaukar da mutanenta ne da Hamas din ke tsare da su ta hayar kaddamar da sabon farmakin na Gaza.
A halin yanzu dai Falasdinawa sun sake zuba ido ga duniya da kuma musamman kasashen Qatar da Masar da Amurka da a baya suka taimaka wajen samar da yarjejeniyar tsagaita wuta don ganin abinda za a yi na kawo karshen sabon tashin hankali da suka fada cikinsa.))