SiyasaAfirka
Harin dakarun RSF a garin Darfur na Sudan ya kashe mutane 24
August 29, 2025Talla
Harin dakarun RSF a arewacin Darfur na Sudan, ya halaka mutane 24 tare da raunata wasu 55, bayan luguden wutar da dakarun kungiyar suka yi wa babbar kasuwar Awlad al-Reef ta birnin el-Fasher.
Wasu likitocin agaji da ake kira da Doctors Network a kasar ta Sudan, sun tabbatar da mutuwar mutanen, bayan hare-haren dakarun RSF a cikin cincirundon jama'a.
Karin bayani:Sudan: Ko yaki ya kawo karshe a Khartoum?
Tun a cikin watan Afirilun 2023 yakin basasa ya barke tsakanin dakarun sojin Sudan masu biyayya ga Janar Abdel Fattah al-Burhan, da na RSF da ke karkashin jagorancin Mohamed Hamdan Dagalo, a korarin bangarorin biyu na kwace ikon kasar.