Mutane 12 sun mutu a wani hari a Filato
January 9, 2020Rundunar 'yan sanda ta Jihar Filaton Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 12 lokacin da wasu mahara suka kai hari a yankin Kombun dake Karamar hukumar Mangu. Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan na Filato Mathias Tyophve ya fitar, ya ce an tura jamai'an tsaro zuwa kauyen da abin ya faru, lamarin da wani shugaban al'umma a karamar hukumar Mangu, Samuel Pukat ya tabbatar.
Wakilin DW Abdullahi Maidawa Kurgwi ya bayyana cewa jama'a da dama na barin yankin Kombun zuwa cikin garin Mangu don guje wa aukuwar wani sabon harin. A halin da da ake ciki dai, kwamandan rundunar soji da ke wanzar da zaman lafiya a jihar Filato, Manjo Janar Agustine Agundu, ya ce sojoji sun kama mutane 7, wadanda ake zargi da marar hannu wajen aikata harin, kuma suna ci gaba da bincike don gano wadanda suka aikata kashe- kashen.