Hari ya kashe masu hakar zinare a Samira na Nijar
May 13, 2025Wasu ma'aikata takwas da ke aikin hakar zinare sun mutu bayan da wani abin fashewa ya tarwatsa motar da suke ciki a Samira da ke yammacin jihar Tillabéri na Jamhuriyar Nijar, inda kungiyoyin masu da'awar jihadi ke fafutuka da makamai. Sai dai jaridar L'Enquêteur mai zaman kanta ta ce adadin wadanda suka mutu ya zarta mutane 10, yayin da majiyoyi na cikin gida suka ce lamarin ya faru ne tun a makon da ya gabata, a yayin da motar da harin ya rutsa da su ta kasance a cikin ayarin da sojoji ke rufa wa baya a kokarin komawa Yamai.
Karin bayani: Lakurawa na zafafa hare-hare a Jamhuriyar Nijar
Babu dai wata kungiya da ta yi ikirarin kai hari a garin Samira, amma wannan ba shi ne karon farko da ake samun asarar rayuka a yankin da ke hada iyakokin Nijar da Mali da Burkina Faso ba. ko a watan Mayun 2023, sojojin Nijar bakwai ne aka kashe a kusa da kauyen Samira mai mahakar gwal, lokacin da daya daga cikin motocin da ke musu rakiya ta taka nakiya. A wannan yanki dai, sojojin Nijar na ci gaba da yakar kungiyoyin masu da'awar jihadi a karkashin shirin Operation Niya main kunshe da sojoji 2,000.