SiyasaGabas ta Tsakiya
Isra'ila tana ci gaba da kai farmaki
March 24, 2025Talla
Wasu hare-haren da Isra'ila ta kaddamar ta sama sun halaka mutane 60 cikin kwana guda da suka hada da mata da yara, a cewar ma'aikatar lafiyar yankin zirin Gaza na Falasdinu.
Karin Bayani: Taron Larabawa kan makomar Gaza a Masar
Isra'ila ta kaddamar da farmaki sakamakon abin da ake gani na gurkushewar yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da kungiyar tsagerun Hamas na Falasdinu. A wannan Litinin kungiyar ta Hamas ta saki faifan bidiyo da ke nuna 'yan Isra'ila biyu da aka yi garkuwa da su tun ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, lokacin da mayakan Hamas suka kai farmaki kan Isra'ila, abin da ya haifar yaki tsakanin bangarorin biyu. Sai dai babu tabbacin lokacin da aka nadi faifan bidiyon.