Hare haren Bam a Rasha
January 24, 2011Wani harin ƙunar baƙin waken da aka kai a filin saukar jiragen sama na Domodevo dake a birnin Mosko na ƙasar Rasha ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama 30 yayin da wasu 130 suka samu raunuka. Kamfanin dillancin labarai na ƙasar ta Rasha Ria Novoti ya shaida cewa ɗan ƙunar baƙin waken wanda ke cikin jama'ar da suka zo tarbon masu balaguron ya tayar da bam din ne a cikin tsakiyar tarin jama'ar. Kwamitin da ke gudanar da bincike akan al'amarin wanda ya ce harin ya na da nasaba da na 'yan ta'ada ya ce wasu abubuwan masu ƙaran gaske sun fashe a cikin zauren da matafiyan ke karɓar adakokinsu.
Shaidu sun ce an yi ta kwasar mutane jina jina bisa branka domin kai su asibiti yayin da wasu ke ta zuba gudu a gigice ta ko'ina jini a jikinsu, Shugaba Dmitri Medeved da ya ɗage ziyarasa zuwa hallarta Taron tattalin arziki a birnin Davos na ƙasar Suizeland.
Yace zama wajibi a ɗauki matakai na musamun a cikin dukanin filayen saukar jiragen saman dakuma tashoshin jiragen ƙasa, ya kuma wakilci ministan sufuri domin ƙaddamarda tsarin. A cikin watan Maris na shekara bara ƙasar ta Rasha ta yi fama da hare hare guda biyu wanda suka kasance mafi muni a cikin shekaru shidda da suka wuce wanda a cikinsu mutane kusan 40 suka mutu waɗanda kuma aka dora alhakinsu akan wasu mata biyu yan asilin arewacin Koreshiya
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Bala