SiyasaSudan
Dakarun RSF sun kashe fiye da mutane 400 a Darfur
April 14, 2025Talla
Rahoton na MDD wanda ya ambato wasu majiyoyi masu inganci, ya ce an yi babban ta'aadi a yankin. Ravina Shamdasani, mai magana da yawun hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ,ta ce sahihan majiyoyi sun bayar da rahoton mutuwar sama da mutane 400. Sudan, kasa ta uku mafi girma a Afirka ta fuskar girman kasa, ta rabu gida biyu tun watan Afrilun shekarar ta 2023. Sakamakon kazamin rikici tsakanin sojojin Janar Abdel Fattah al-Burhan, wanda ke mulkin kasar tun bayan juyin mulkin shekarar ta 2021, da dakarun tsohon mataimakinsa, Janar Mohamed Hamdan Daglo. Kawo yanzu rikicin ya haifar da raba mutane miliyan 13 da suka hada da ‘yan gudun hijira miliyan takwas da matsugunansu.