Dakile ta'addanci a Najeriya
May 7, 2025Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa tana daukan sabbin matakai don dakile sake bullar kai hare-hare na kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya da ma wasu kungiyoyin yan ta'ada da suka bulla a jihohin Niger da Kwara, inad ta ce an samu gaggarumin ci gaba a kokarin samar da tsaro a kasar.
Karin Bayani: Najeriya: Shirin sauya tunanin barayin daji
Kokari ne dai na katse hanzarin kungiyoyin ‘yan ta'ada da kje kai hare-hare a sassan Najeriyar wanda gwamnatin Najeriyar ta bayyana cewa ta fara samun nasara na maido da zaman lafiya musamman tafiye-tafiye a kan wasu manyan hanyoyin kasar da a baya suka zama hanyar garkuwa da ja,a'a domin neman fansa. Ministan tsaro na Najeriya Mohammed Badaru Abubakar da ya sanyawa ‘yan jaridu faifan bindiyo na mutanen da suka ba da tabbacin samun wannan sauki har da murnar tunkarar shirin noma a daminar bana. To sai dai a 'yan watanin nan an ga sake bullar kai hare-hare na ta'adanci musamman a jihohin Borno da Yobe a yanayin da ke tada hakali sosai.
Rashin samun zaman lafiya a kasar Siriya na zama wata sabuwar barazana ta watsuwar makamai da ma ‘yan ta'adda kamar yadda ya faru a lokacin da tsohuwar gwamnatin Libiya ta rushe. Wannan ya kara zama abin dubawa sanin halin da ake ciki a yanzu da kasashen Mali da Jamhuriyar Nijar suka fice daga kungiyar ECOWAS, kasashen da ke da muhimmanci sosai ga zaman lafiyar Najeriya.
Dakile hanyoyin da ‘yan ta'adda ke samun makimai da abubuwa masu fashewa da suke kai hari a kan jama'a a Najeriya da kasashen Afrika muhimmi ne a wannan mataki. Mohammed Sanusi jami'i ne a ofishin mai baiwa shugaban Najeriya shawara fanin tsaro.
Najeriya dai ta bayyana cewa ta samu nasarar dakile sabuwar kungiyar da ke kai9 hare-hare da Mamuda a jihohin Kwara da Niger, sai dai har yanzu ana ci gaba da fuskantara yiwa jama'a dauki dai dai a wasu sassan Najeriyar, tare da zargin ganinwasu fafaren fata cikin aikata ta'asa da karkashe jama'a musamman a jihohin Benue da Plato da gwamnonin suka kai ga ambata hakan.