SiyasaTurai
Armeniya da Azerbaijan sun hau kan teburin sulhu
October 9, 2020Talla
A karon farko kasashen Armeniya da Azerbaijan da ke fada da juna, sun amince sun hau kan teburin sulhu a wannan Juma'a, wakilan kasashen biyu sun shiga tattaunawar da Rasha ta shirya a birnin Moscow, ba a dai kai ga sanin yadda za ta kaya ba amma masu sharhi na ganin akwai yiyuwar a lalubo hanyar dakatar da fadan da yayi sanadiyar rayuka da dama.
Wannan rikicin kan yankin Nagorno-Karabakh ya fara kunno kai tun bayan rushewar tsohuwar Tarayyar Soviet, inda kasashen suka fara kai ruwa rana tun farkon shekarun 1990. Tun a wancan lokacin ake samun barkewar rikici lokaci zuwa lokaci. Amma mafi muni shi ne rikicin 'yan kwanakin nan.