Matakan warware rikicin Rasha da Ukraine
August 21, 2025Shugaba Vladimir Putin na Rasha yana shirye-sjiryen ganawa da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelenskiy amma idan an dauki matakan magance duk batutuwan da suke haifar da sabani tsakanin bangarorin biyu, kamar yadda ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya bayyana. A makon da ya gabata Putin ya gana da Shugaba Donald Trump na Amurka kan batun na samar da mafita a yakin da ke faruwa tsakanin kasashen Rasha da Ukraine.
Karin Bayani: Trump ya gana da wasu shugabannin Turai
Daga bisani kuma Shugaban na Amurka ya gana da shugaban Ukraine gami da shugabannin wasu manyan kasashen Turai. Yanzu jami'an Rasha suna nuna damuwa idan wani shugaban Ukraine na gaba zai amince da duk wata yarjejeniyar da Shugaba Zelenskiy na Ukraine zai saka hannu a kai, ganin a hukumance wa'adin mulkinsa ya kare.