Hankula sun kwanta bayan jawabin Sarki
March 27, 2025Da fari dai dukkan sarakunan da ke takaddama akan masarautar sun bayyana aniyar su ta yin hawan sallah wanda da ake gani zai iya kawo tashin hankali da arangama a tsakanin magoya baya lamarin da ya jawo shiga tsakani daga rundunar tsaro a jihar Kano
Har yanzu dai babu takamaimen dalilin da ya sanya kwatsam aka jiyo Sarki Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi jawabin janye kudirinsa na hawan sallah, sai dai a jawabin nasa ya bayyana cewar janyewar ta biyo bayan nasihohi da ya samu daga wasu da ya ke girmamawa da kuma neman dawwamammen zaman lafiya a jihar
Bashir Hayatu jantile na daga cikin manyan hadiman Sarkin Kano Muhammad Sunusi na biyu ya ce sun ji dadin wannan kalamai na mai martaba sarki Aminu Ado Bayero sai dai ya ce dama can tun wuri ya kamata a ce ya dauki irin wannan mataki.
To amma ga mutane irin su Ibrahim Ado Kurawa masanin tarihin masarautar Kano, ya ce ai dama tun ran gini tun ran zane domin sarki daya ne ke yin hawa a tarihin Kano kuma sai wanda ya ke zaune a gidan Rumfa
Wannan rikici na masarauta dai ya dade yana jawo wa jihar Kano asara la akari da yadda aka tasamma zubar da darajar masarautar, da yada kalaman cin fuska ga sarakuna ga uwa uba girke jami'an tsaro masu yawa a gidan sarki na nasarawa daidai lokacin da ake bukatar su a cikin gari inda yan daba ke cin karansu babu babbaka.
Har wannan lokaci dai rundunar yan sanda bata bayyana matsayin irin shirin da ta yi ba na tabbatar da tsaro da ma matsayin yadda ta ke kallon hawan,tun da fadar Muhammad Sunusi na biyu bata bayyana janye hawan ba.