Hambararren shugaban Gabon ya samu mafaka a Angola
May 16, 2025Fadar shugaban kasar ta wallafa hotunan Ali Bongo Ondimba ya isa Luanda babban birnin Angola, a shafinta na Facebook.
An ce sakin Bongo da matarsa da dansu, ya biyo bayan wata yarjejeniya tsakanin shugaban Angola Joao Lourenco da sabon shugaban Gabon Janar Brice Oligui Nguema, wanda ya hambarar da Bongo kusan shekaru biyu da suka shige, aka kuma ayyana a matsayin wanda ya lashe zabe a watan jiya.
Kungiyar Tarayyar Afirka da sauran kasashen duniya sun yi kira da a saki iyalin Bongo kuma Shugaba Lourenco na Angola da ya yi shugabancin AU na gajeren lokaci, yayi amfani da damar wajen cimma yarjejeniyar sakin na sa, kamar yadda ofishinsa ya nunar.
An yi wa Bongo daurin talala bayan juyin mulkin na watan Agustan 2023. amma bayan mako guda aka sake shi saboda dalilai na rashin lafiya, a cewar mahukuntan kasar Gabon. Sai dai magoya bayansa sun musanta sakin na sa, inda ake ci gaba da kula da dukkan motsinsa.