Hamas ta amince da sabon tayin tsagaita wuta a Gaza
March 30, 2025A wani sako da guda daga cikin shugabannin Hamas ya fidda na cewar sun amince da tayin tsagaita wuta da bangarorin dake shiga tsakani suka gabatar musu, kuma suna fatan Isra'ila za ta mutunta duk wasu sharudan dake kunshe a yarjejeniyar.
An sake komawa teburin tattaunawa ne jim kadan bayan da Firaministan Isra'ilaBenjamin Netanyahu ya yi barazanar mamaye wani yanki na Gaza idan Hamas bata sako al'ummarsa ba, a nata martanin Hamas ta ce muddin hakan ta faru to kuwa hakan zai zamo sanadin rayukan mutanen.
Makonni biyu ke nan da sojojin IDF suka koma kai farmakinsu a Gaza, inda dukkanin bangarorin biyu ke fuskantar munanan bore daga al'ummarsu, Falasdinawa na masu kiran Hamas da ta fice daga wasu yankunansu da ma Isra'ilawa dake kiran mahukunta na Tel Aviv dasu amince da yarjejeniyar da za ta sako 'yan uwansu da ke Gaza.
Karin BayaniIsra'ila ta lashi takobin ci gaba da mamaye Gaza :