Halin da 'yan gudun hijira ke ciki a Kenya
November 15, 2011Hukumar kula da masu gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce barkewar cutar amai da gudawa ta kwalera wanda har ya kai ga rasuwar mutun guda a sansanin 'yan gudun hijiran Dadaab da ke Kenya ya fara barazana ga nasarar yunkurin da masu aikin agaji ke yi a wurin don kawo karshen matsalar yunwan da ta addabe wadanda ke samun mafaka a sansanin.
A wannan talatar ce hukumar da ke da shelkwatarta a Geneva ta ce wasu gwaje-gwajen da ta yi, ya tabbatar da barkewar wannan anobar.
Kakakin hukuwmar Andrey Mahechic ya fadawa kamfanin dillancin labarun Associated Press cewa rashin tsaro da ma yawan tashin bama-bamai, kamar irin wanda aka samu a sansanin a watan da ya gabata, da kuma yawan ruwan sama na cigaba da zama kalubale wajen aiwatar da ayyukan agaji a yankin. Bayan da aka yi wata guda yanzu da sace wasu ma'aikatan agaji uku daga sansanin Mr Mahechic ya kara da cewa an sake sace akalla 'yan sandan Kenya 100 a watan da ya gabata kawai wadanda ke tabbatar da tsaro a sansanin
Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar