Aikin hajjin bana ya kasance gagarumi. A tarihin wannan ibada da mabiya addinin Islama ke yi a duk shekara, ba a taba samun adadin mutane fiye da miliyan biyu da rabi da suka halarci wannan ibada kamar a wannan shekara.
Mutane fiye da miliyan biyu da rabi suka halarci wannan ibada a wannan shekara daga ko'ina a kassahen musulmi na duniya jama'a sun halarci aikin na haji wanda ya sha bam-bam da sauran aikin hajjin na shekararun baya.