Habasha ta gaza binciken faduwar jirginta
March 13, 2019Talla
Jami'an kamfanin jirgin Ethiopain Air sun ce matakin ya biyo bayan karancin na'urorin tabbatar da sahihancin binciken akwatin nadar bayanan jirgin, ana sa ran kasar Amirka ko kasar Turai da tafi kusa Habasha ne za su gudanar da aikin binciken faduwar jirgin.
Tun bayan hatsarin jirgin da ya yi sanadiyar rayukan mutane 157, kasahen duniya sun dena aiki da samfurin jirgin. Wasu kasashe ke hana irin jiragen ketawa sararin samaniyar kasashensu.