Gwamnoni sun koka kan yadda hare-hare ke barazana ga noma
June 10, 2025Sabbin hare-hare da mayakan Boko Haram da ISWAP ke kaiwa a sassan jihohin Arewa maso gabashin Najeriya da kuma tashin hankali da ake samu a yankin Arewa ta Tsakiya na neman hana manoma fita gonakinsu, a daidai lokacin da damuna ta fara kankama a kasar. Wannan ne ya sa gwamnaonin yankin Arewa karkashin jagorancin shugaba su kuma gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya suka bayyana damuwa saboda yadda matsalolin tsaron ke neman hana manoma zuwa gonakinsu, lamarin da ka iya haifar barazanar karancin abinci da hauhawar farashin kayan masarufi.
Wani maomi ya bayyana halin da yake ciki dangane yadda matsalolin tsaro ke haifar musu da tarnaki na zuwa gonakin inda ya ce: "Kullum Boko Haram, bayan kwana biyu, uku, suna zuwa karbar kudi, suna kashe mutum, ba zai wuce sati daya ba, sai Boko Haram sun fita, sun je gonan ma suna gudu suna zuwa."
Karin bayani: Yaushe za a shawo kan matsalar tsaron Najeriya?
Su ma shugabannin kungiyoyin manoma sun nuna damuwa kan halin da ake ciki, inda suka ce in ba an tashi tsaye ba, da kamar wuya a iya magance matsalolin 'yunwa da tsadar abinci kamar yadda Hon Muhammad Magaji, sakataren kungiyar manoma ta Najeriya wato AFAN ya ce: "Tabbas! akwai matsalar tsaron a arewacin Najeriya, kuma lallai za ta hana noma, domin yanzu ne yawancin wurare ke yin shuka. A wuraren da duk ake da matsalar rashin tsaro, za ka samu ba abin da aka yi, ko sharar gona ba a yi ba saboda wannan matsalar. Ya kamata a yi tsayuwar daka kan abin da gwamnati ta dauko cewa yaki da barayin daji da Boko Haram don a tabbatar da cewa manoma sun yi noma: Wannan shi ne ya kamata a yi da hanzari ba tare da bata lokaci ba.”
Karin bayani:Sabon yanayi na tabarbarewar tsaro a Najeriya
Don magance wannan matsalar tsaro, gwamnonin na shirin hadin gwiwa, inda za su hada kai da sarakunan gargajiya, shugabannin tsaro, da kungiyoyin farar hula domin bullo da sabbin tsare-tsare na samar da zaman lafiya. Gwamnan Muhammadu Inuwa Yahya ya ce: "Tsaro shi ne kusan na farko kuma yanzu shi ne ya fi damun mu kuma ita kan ta gwamnatin tarayya tana dame da yadda za a yi. Amma ya ya za a yi da kuma wa za a yi? Wannan y na bukatar tuntuba ne a kullum, shi ya sa za ka ga muna yawan zama a kullum, kuma kowa ka yi magana kan matakin da ake dauka, Dole ne mu hada karfi da karfe, mu yi dabarun da za a yi mu samu tsaro, mu samu zaman lafiya.”
Rashin noma saboda matsalartsaro, ba waijihohin arewacin Najeriya kadai zai shafa ba, amma har da sauran sassan kasar, lamarin da ke iya haifar da matsin tattalin arziki da wahalar rayuwa a fadin kasa.