Najeriya: Takaddama kan sulhu da 'yan Boko Haram
August 23, 2021Rahoton da wasu hirarraki da masu ruwa da tsaki kan batun ko bayan kungiyoyi na farar hulla, sun ce an kai ga cimma yarjejeniya a tsakanin manyan 'ya 'yan kungiyar domin ajiye makamai tare da sake komawa al'umma da nufin kaiwa ga rayuwa mai amfani, a yayin da ita kuwa gwamnatin Abuja a cewar majiyoyi za ta kau da kai ga hukuncin daruruwan 'yan kungiyar ke fuskanta cikin kasar.
A kalla mambobin kungiyar sama da 150 ne suka mika wuya suka kuma shiga wani shirin na sauya tunani na watanni shida da jami'an tsaron Najeriya ke jagoranta. To sai dai kuma shirin sulhun na daukar hankali a ko ina a fadin kasar a tsakanin masu yi masa kallon hanyar kai karshen yakin, da kuma masu kallonsa a matsayin kokarin cin fuska ga dubban mazauna yankin Arewa maso gabashin Najeriya da kungiyar ta tilastawa rayuwa maras dadi.
Karin Bayani: Yadda jama'a ke tserewa saboda fargabar hare-hare
Sanata Ali Ndume dan majalisar dattawa daga Borno, kuma daya a cikin wadanda Boko Haram ta yi wa ba dadi a baya ya ce "Batun na sulhu na kamar cin fuska ne ga mutanen da 'yan Boko Haram suka ci zarafinsu: Yadda jama'a ke tserewa saboda fargabar hare-hareri na harba bindiga ne a cikin ruwa."
Dokar yaki da ta'addanci a Najeriya ta tanadi hukunci mai karfi ga 'yan kasar dama baki da aka samu da ruwa da tsaki ko aikata laifi a cikin yakin ta'addaci. Sai dai ga Kabir Adamu da ke zaman kwararre bisa harkar tsaro ya ce "Sulhu na zaman wani bangare na kokarin kai karshen yakin da ya share shekaru 12 amma kuma aka kasa kaiwa zuwa gaci."
Karin Bayani: Rashin tsaro ya dakatar da aikin Majalisar Dinkin Duniya
Ra'ayi sun banbanta a cikin tarrayar Najeriya, inda wasu ke kallon sulhun na iya kaiwa ya zuwa karshen yakin da aka jima ana yi, hakan da masu yi masa kallon kokari na cin fuskar 'yan kasar da suka yi hasarar rayuwa da dukiya sakamakon wannan yakin. Sanata Ahmed lawal shugaban majalisar dattawan Najeriya cewa ya yi "Akwai bukatar yin taka tsan-tsan da nufin tantance aya da tsakuwa a kokarin fuskantar makomar mayakan kungiyar ta Boko Haram."
Sama da mutane 35,000 ne suka halaka baya ga wasu fiye da miliyan biyu dake gudun hijira samakon yakin da ya shafe shekara da shekaru ana gwabzawa, kana ya sa Najeriya ta yi kaurin suna a duniya wajen matsalar rashin tsaro.