Lebanon na shirin kwancewa Hezbollah damara
August 6, 2025Gwamnatin Lebanon ta umurci rundunar sojin kasar a ranar Talata da ta fara shirin kwancewa kungiyar Hezbollah damara kafin karshen wannan shekara ta 2025, matakin da ba a taba ganin irinsa ba tun bayan yakin basasar kasar.
An dauki wannan mataki ne a yayin zaman taron majalisar ministocin Lebanon, a daidai lokacin da tasirin kungiyar mai kusanci da Iran ke kara disashewa a fagen siyasar kasar bayan rage mata karfi da Isra'ila ta yi a lokacin sanhin hunturun bara.
Har ila yau matakin kwancewa Hezbollah damara na daga cikin tanade-tanaden yarjejeniyar tsagaiata wuta da Amurka ta jagoranta wadda ta kawo karshen yaki a tsakanin kungiyar da Isra'ila a ranar 27 ga watan Nowamban bara.
Sai dai tuni a wani jawabi da aka watsa ta gidan talabijin shugaban kungiyar ta Hezbollah Naim Qassem ya ce ba zai lamunci duk wata ajandar kuncewa mayakansa damara ba a karkashin matsin lambar Isra'ila.