Guinea-Bissau: Embalo ya ki sauka daga mulki
March 5, 2025A ranar 28 ga watan Fabrairun 2025 ne wa'adin mulkin shekaru biyar na Embalo ya kare a matsayin shugaban kasa. A bisa doka dai ya tashi daga zama shugaban Guinea-Bissau, amma ya ki sauka. Domingos Simoes Pereira, shugaban jam'iyyar Afirka ta kwatar 'yancin Guinea da Cape Verde (PAIGC) ya ce dole ne Embaloya sauka ba tare da wani bata lokaci ba.
Pereira na jagorantar hadakar Jam'iyyun da suka lashe zaben majalisar dokokin da aka yi a shekarar 2023 da gagarumin rinjaye. To amma tun daga wancan lokaci Embalo ya hana Pereira kafa gwamnati.
Haka ita majalisar dokoki wa'adinta na shekaru biyar sun kare, a saboda haka Pereira yana so a gudanar da sabon zaben shugaban kasa da na majalisun dokoki cikin kwanaki 90 sabanin ranar 30 ga watan Nuwamba da shugaban kasar ya sanar.
Pereira ya kara da cewa wannan shi ne abin da kundin tsarin mulki ya tanadar. Majalisar da shugaban kasar ya rusa ta 2023 dole a yi gaggawar dawo da ita. A cewar Pereira wannan majalisar ce za ta zabi yan hukumar zabe ta kuma zabi shugaban kotun tsarin mulki wacce ita ma wa'adinta ya kare. Jam'iyyu da dama dai a kasar da kwararrun masana shari'a da wakilan kungiyoyin farar hula a Guinea Bissau na da wannan ra'ayi.
Nuno Nabiam tsohon firaminista kuma kuma shugaban jam'iyyar adawa ta biyu mafi girma API ya shaida wa DW cewa zanga zanga ba makawa har sai an dawo da tafarkin doka.
"Ya ce zanga zanga kam babu makawa. Dole ne al'amura su tsaya cik a kasa har sai an maido da tsarin doka. Dole ne a kare kundin tsarin mulki. Na yi imani da haka."
Wasu 'yan Guinea-Bissau da ke kasashen waje sun gudanar da zanga zanga inda suke kiran a martaba kundin tsarin kuma Embalo ya sauka.
Wannan wasu yan Guinea-Bissau da ke zaune a Lisbon kasar Portugal suke zanga zanga tare da kiran a bi doka a kasarsu. Suna cewa tun da wa'adin mulkin Sissoco Embalo ya cika to ya kamata ya sauka cikin girma da arziki don ci gaban dimukuradiyya.
Embalo dai na mulki kasar ta yammacin Afirka ne a yanzu tare amfani da dokoki na musamman fiye da shekara daya kenan, kuma bisa ga dukkan alamu ya kudiri aniyar taka wa Domingos Simoes Pereira birki, inda gwamnatin ta zarge shi da cin hanci ta kuma sha alwashin ba za a nada shi firaminista ba.
Wakilin Domingos Simoes Pereira na Jam'iyyar PAIGC a nan Jamus Pedro Jandim ya yi tsokaci kan wannan dambarwa yana mai cewa:
"Muna da shugaban kasa ne wanda bai damu da matsalolin da jama'arsa ke ciki ba a gida, yana harkokinsa kawai a waje. Makarantuda asibitoci ba sa aiki. Babu hanyoyi komai ba ya aiki a Guinea-Bissau."
A yanzu dai yadda lamura ke gudana Embalo na so ya ci gaba da zama shugaban kasa har tsawon wani lokaici a nan gaba, da kuma hana sauran jam'iyyu in banda ta sa da kuma mutanen da ya zaba ya nada a gwamnati, babu mai iya samun karfin ikon gudanar da komai. Embalo wanda tsohon Janar ne na soja ya yi firaministan Guinea-Bissau tsakanin 2016 da 2018. Kuma a da dan Jam'iyyar PAIGC ne kafin daga bisani ya shiga jam'iyyar MADEM G15 wadda ta balle.
Sai dai kuma Umaro Sissoco Embaló ya baiyana 'yan adawar a matsayin wadanda basu san komai ba, inda ya sa kafa ya yi ficewarsa ya tafi wajen Vladimir Putin a Moscow.
Ministan cikin gida Botche Candé daya daga cikin na hannun daman Embalo ya yi barazanar cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wata zanga zanga ba yana mai cewa Jami'an tsaro za su mukrkushe dukkan wani yunkuri na tada zaune tsaye a kasar.
A halin da ake ciki dai yanzu a Guinea-Bissau ana zaman dar dar. An baza sojoji a tituna yayin da al'uma suke cikin fargabar abin da ka iya faruwa a nan gaba.
Tawagar ECOWAS karkashin jagorancin jami'in diflomasiyyar Najeriya Ambassador Bagudu Hirse ta kai ziyara Bissau sai dai tuni suka koma bayan da Embalo ya yi barazanar korarsu kafin ya tashi zuwa Rasha. A cewar Bubacar Ture shugaban hadakar kungiyoyin kare hakkin bil Adama a Guinea-Bissau ya ce ba sa ganin ECOWAS za ta iya yin wani tasiri wajen magance rikicin.