You need to enable JavaScript to run this app.
Tsallake zuwa shafin jadawali
Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bidiyo
Shirye-shiryen DW Hausa
Yankuna
Najeriya
Nijar
Afirka ta Yamma
Sassa
Siyasa
Zamantakewa
Wasanni
Mayar da hankali
Ilimin Fasahar Zamani
Shirye-shiryen DW Hausa
Bidiyo
Talabijin kai tsaye
Talla
Guguwar Neman Sauyi
Guguwar neman sauyi ta kada a kasashe da dama na Larabawa inda mutane suka bukaci sauyin shugabanci.
Tsallake zuwa bangare na gaba Duk abin da ya shafi wannan maudu'i
Duk abin da ya shafi wannan maudu'i
Martanin 'yan Masar kan takarar Al-Sisi
Al'ummar Masar na ci gaba da nuna goyon bayansu ga takarar Abdulfatah al-Sisi wanda bayan an yi mi shi ƙarin girma, ana sa ran zai ajiye aikin soji ya shiga siyasa
Sosoji a Masar sun amince da takarar Al-Sissi
Sojojin kasar Masar sun bada amincewarsu ga takarar Janar Abdel Fattah al-Sissi, a matsayin dan takara a zaben shugaban kasar da za a yi nan gaba a kasar.
Mutane kusan 30 sun hallaka a kasar Masar
Rikicin da ya barke a kasar Masar tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga ya yi sanadiyar mutuwar mutane masu yawa
Jirgin sama mai saukar ungula na sojojin Masar ya fadi
Wannan ya hadari ya afku ne yayin da ake tunawa da shekaru uku da fara boren da ya kawo karshen gwamnatin Hosni Mubarak ta kasar Masar
Ruwan bama-bamai a kasar Masar
Mutane shida sun hallaka a kasar Masar bayan da wasu bama-bamai hudu sukia tashi a Alkahira babban birnin kasar.
Tashin bama-bamai sun ruɗa birnin Alƙahira
A kasar Masar an samu fashewar wasu ababai da ake kyautata zaton bam ne a gaban hedkwatar rundunar 'yan sandan da kuma a tashar jiragen ƙasa a babban birnin ƙasar.
Rigingimu da cin zarafin 'yan adawa sun karu a Masar inji Amnesty
Kungiyar Amnesty International ta bayyana cewa Masar ta shiga wani yanayi na tashe-tashen hankula maras misali, tun bayan da sojojin kasar suka kifar da gwamnatin Mohamed Morsi.
Ƙuri'ar raba gardama na gudana a Masar
Mutune 5 sun rasu, yayin da jami'an tsaron Masar suka fasa wani gangamin masu adawa da juyin mulkin soji, lokacin da 'yan ƙasar ke kaɗa ƙuri'ar raba gardama bisa kundin tsarin mulki
Zanga-zanga a Masar kan Mursi
An dage sauraron karar tsohon Shugaban Masar Mohamed Mursi
Rikicin Masar na daukan sabon salo
Dalibi daya ya rasa ransa cikin artabu tsakanin jami'an tsaron kasar Masar da masu zanga-zangar.
Rikicin Masar ya zafafa
Mutane uku sun hallaka yayin dauki ba dadi tsakanin jami'an tsaron Masar da masu zanga-zanga.
Hukumomin Masar sun tsare mutane da yawa karkashin dokar yaki da ta'addanci
Tun bayan harin kunar bakin wake da aka kai kan wata shelkwatar 'yan sanda da ke birnin Mansura, mahukuntan birnin Alkahira ke matsa lamba kan masu kishin Islama.
Mutane da yawa sun rasu a wani harin bam a shelkwatar 'yan sanda a Masar
Hukumomin kasar sun kuduri aniyar zakulo wadanda ke da hannu a harin don gurfanar da su gaban kuliya.
Tsugune ta ki karewa a Masar
Wani harin Bom da aka kai a kasar Masar ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 14 tare kuma da jikkata wasu da dama.
Shari'ar masu adawa da Mubarak a Masar
Kotun Masar ta yanke hukuncin dauri a gidan maza a kan wasu da suka shiga zanga zangar da ta yi sanadin hambarar da gwamnatin Hosni Mubarak a shekara ta 2011.
Belin masu zanga-zanga a Masar
An bada belin wasu matasa da aka yankewa hukuncin kwanaki 15 a gidan kaso, bayan da suka gudanar da zanga-zanga a Masar.
Saɓani kan sabon tsarin mulki na Masar
Akwai sauran aiki kan rubuta sabon kundin tsarin mulkin ƙasar wanda ake ta yin tankiya akai
Keta dokar tsarin zanga-zanga a Masar
Magoya bayan Kungiyar 'yan Uwa Musulmi sun gudanar da jerin gwano a garuruwan Masar da dama da nufin yin buris da dokar neman izini kafin gudanar da zanga-zanga.
Nuna rashin amincewa da sabuwar dokar Masar
Shugaban Masar ya amince da dokar da ta takaita taron mutane a cikin kasar.
Masar ta kori jakadan Turkiyya da ke kasar
Kasar Masar ta bada sanarwar korar jakadan Turkiyya da ke kasar Huseyin Avni Botsali bayan da ta ce fira ministan Turkiyya ya yi kalamai marasa dadi ga gwamnatin Masar.
Gwamnatin Masar na fuskantar ƙalubale
Jami'an tsaron ƙasar Masar sun yi amfani da ƙarfi wajen wargaza masu nuna adawa da gwamnatin ƙasar.
Martani kan cire dokar ta ɓaci a Masar
Mahukuntan Masar sun mutunta hukuncin Kotu sun cire dokar ta ɓaci a ƙasar, sai dai wasu 'yan ƙasa na ganin cewa an ɗauki matakin dan daɗaɗawa ƙasashen yamma ne
Gwamnatin Masar ta cire dokar ta baci
Mahukutan kasar Masar sun ce za su mutunta hukuncin kotu kan kawo karshen aiki da dokar ta baci.
Gurfanar Morsi a gaban kotun Masar
Ana samin ƙaruwar tashin hankali a Masar a daidai lokacin da ake fara shari'ar tsohon shugaba Morsi, abin da ya sa aka tsaurara tsaro a birane da dama na wannan ƙasa.
A ƙasar Masar tarzuma na ƙara bazuwa
An samu tashe-tashen hankula a yankunan Isma'iliya da Sinai, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Hulɗa tsaro tsakanin Amirka da Masar
Yayin da Ƙungiyar Tarrayar Turai ta dakatar da ba da tallafin tsaro ga Masar, Amirka na ci gaba da bai wa ƙasar tallafi .To amma shugaba Barack Obama ya ce za su sake nazari.
Mutane 28 sun rasu a zanga-zangar Masar
Kimanin mutane 28 ne hukumomin Masar suka ce sun rasu sanadiyyar wani rikici da ya biyo bayan zanga-zangar da magoya baya da masu adawa da shugaba Mursi suka yi.
Masar ta yi gargadi ga masu zanga-zanga
Mahukuntan Masar sun gargadi al'ummar kasar da suka daura aniyar yin zanga-zanga a kasar a ranar Lahadi da su guji yin hakan ko su fuskanci fushin hukuma.
Masar ta haramta ayyukan kungiyar 'Yan uwa Musulmi
Ko da yake ana iya daukaka kara don kalubalantar wannan hukuncin, amma duk haka ya bude wa hukumomi kofar bin diddigin ayyukan jin kai da kungiyar ke yi.
Gargadin sojojin Masar ga masu bore
Gwamnatin kasar Masar ta jaddada aniyarta ta sa kafar wando guda da masu boren yin Allah wadai da juyin mulkin matikar suka ci-gaba da gurganta harkokin sufuri.
Yaki da masu tada tarzoma a Masar
A yayin da Masar ke kai hari don kawar da masu tada tarzoma a Sina'i , wata kungiya a yankin ta dauki alhakin neman kissan wani jami'i a kasar.
Martani kan harin minista a kasar Masar
'Yan adawa da ke ci-gaba da nuna rashin goyon bayansu ga juyin mulkin da soji suka yi a Masar sun nuna rashin amincewarsu da harin da aka kai wa ministan cikin gidan kasar.
Harin bama-bamai a Masar
Ministan cikin gida na ƙasar Ibrahim Muhammed ya ƙetare rijiya da baya a wani harin bam wanda aka kai a kan ayerin motocin da ke yi masa rakiya.
Tasirin rikicin Masar ga 'yan gudun hijirar Afirka
'Yan gudun hijirar Afirka na fama da matsaloli daban daban a yunkurinsu na tsallaka wa zuwa Isra'ila domin samun aikin yi.
Zirin Gaza na cikin kaduwa tun bayan juyin mulki a Masar
Juyin mulkin da aka yi a Masar ya matukar shafar makwabciyarta Zirin Gaza, inda yanzu daruruwan mutane ba sa iya fita daga yankin domin an rufe kan iyakarsa da Masar.
Faragabar kiristoci 'yan koptik a Masar
Kiristoci mabiya darikar Koptik na nuna damuwa game da tashen-tashen hankula da ke ritsawa da wurarensu na ibada da dukiyoyinsu tun bayan da aka hambarar da Mohamed Morsi daga karagar mulkin Masar.
Wata kotun kasar Masar ta ba da umarnin sakin Mubarak
A ranar Alhamis ake sa ran sakin tsohon shugaban na Masar saboda a cewar lauyansa babu wasu dalilai na ci gaba da tsare Hosnui Mubarak din.
Zargin kasashen yammacin duniya da nuna halin ko-oho ga rikicin Masar
Bangarorin da ke fito na fito a Masar, sun cimma daidaito wajen nuna fushinsu ga manufofin kasashen yammacin duniya game da rikicin kasar.
Neman a bincike take yancin ɗan Adam a Masar
Ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa na neman sai hukumomin Masar su bar jami'an ƙasashen waje, su gudanar da binciken cin zafarin jama'a
EU za ta yi taro kan rikicin Masar
Kungiyar Tarayyar Turai ta EU za ta gudanar da wani taro a ranar Laraba mai zuwa don duba halin da Masar ta shiga tun bayan da soji su ka hambarar da gwamnatin Mursi.
Illar tashin hankali ga tattalin arzikin Masar
Rikicin siyasa tare da zubar da jini a Masar, yana haddasa mummunar illa ga tattalin arzikin kasar da ta dogara ga maziyarta daga ketare.
Shawarar kwamitin sulhun MDD ga Masar
Manbobin 15 na Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da suka y zama na musamman sun yi kira ga bangaraorin Masar da ke gaba da juna da su kai hankali nesa.
Kasashen duniya sun yi Allah wadai da kissan masu bore a Masar
Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai, da kuma kasashen duniya daban daban na yin suka ga matakan da dakarun tsaron Masar ke dauka a kan magoya bayan Mursi.
An kafa dokar ta-ɓaci a faɗin ƙasar Masar
An hallaka mutane da dama a ci-gaba da matakan amfani da ƙarfi, don tarwasta magoya bayan Mursi,
An tarwatsa magoya bayan Morsi a Masar
Magoya bayan tsohon shugaban Masar Mohamed Morsi da masu adawa da shi sun yi fito na fito tsakaninsu. Lamarin da yasa 'yan sanda amfani da karfi wajen shiga tsakani.
Masu zanga-zanga a Masar na nuna turjiya
Magoya bayan Mursi na ci gaba da nuna turjiya duk da barazanar gwamnati na kwashe su daga sansanonin da suke zaman dirshen da ƙarfi da yaji
Rikicin siyasar Masar na daukan sabon salo
Gwamnatin Masar na shirin daukar matakin tarwatsa masu zanga-zangar goyan bayan hambararren shugaban kasa Mohamad Mursi
Isra'ila ta rufe filin jirgin samanta dake kan iyaka da Masar saboda dalilan tsaro
Rufe filin jirgin saman na birnin Eilat dake a Tekun Bahar Maliya na da nasaba da karuwar aikace-aikacen masu kishin addinin Islama a Sinai dake makwabtaka.
Rikicin kasar Masar ya tsananta
Ana ci-gaba da kai ruwa rana tsakanin 'Yan Uwa Musulmi da sojoji sama da wata guda da hambarar da gwamnatin zababben shugaban kasar Masar Mohammed Mursi.
Rikicin Masar na ƙara yin muni
Gwamnatin ta ce za ta yi amfani da ƙarfi wajen kawo ƙarshen zanga-zanga da zaman durshin da magoya bayan Mursi ke yi.
Shafin da ya wuce
Shafi 12 daga 18
Shafi na gaba