Guguwa ta katse wutar lantarki a Amurka
March 14, 2023Talla
Guguwa da iska mai karfin gaske sun haddasa katsewar wutar lantarki a yankin na arewa maso gabashi inda lamarin ya shafi gidaje sama da dubu 240,000. An rufe makarantu a Jihohin Massachusetts inda masu bincike sararin samaniya suka yi hasashen cewar za a samu zubar dusar kankara da tsayinta zai iya kai sentimeta 60, da kuma a New Hampshire,inda aka dage zaben kananan hukumomi da dama da aka shirya yi a ranar Tala(14-03-23).