Guguwa ta halaka sama da mutum 20 a Amurka
May 17, 2025Wata bakar guguwa mai matukar gigitarwa ta halaka sama da mutum 20 a jihohin Missouri da Kentucky na Amurka, a cewar hukumomin kasar.
Gwamnan jihar Kentucky, Andy Beshear, ya wallafa a shafinsa na X cewa akalla mutane 14 ne suka mutu sakamakon guguwar da ta afku a daren Juma'a, sai kuma wasu bakwai a Missouri, a cewar jami'an yankin.
Guguwa ta sa Joe Biden dage ziyararsa zuwa Jamus da Angola
Hotunan da aka dauka ta hanyar amfani da kyamara mai tashi sama da kafofin yada labaran yankin suka wallafa sun nuna barnar da aka samu a garin London na Kentucky, inda gidaje suka rushe.
Gwamnan ya kara da cewa sama da mutane dubu 100 a jihar sun rasa wutar lantarki, kuma gundumomi biyar sun ayyana dokar ta-baci.
COP29: Kalubalen sauyin yanayi na duniya
Gabashin Kentucky, yankin da aka sani da hakar ma’adinan kwal, guda ne daga cikin yankuna mafiya talauci a kasar Amurka.
Mutane biyar sun mutu a babban birnin Missouri, St. Louis, sai kuma biyu a gundumar Scott, in ji wata sanarwa da rundunar ‘yansandan jihar ta fitar.