Gomman Falasdinawa sun mutu wajen jiran kayan agaji
July 20, 2025Rahotanni daga Zirin Gaza sun yi nuni da cewa, kimanin Falasdinawa 30 ne suka mutu yayin da wasu 60 suka jikkata a wani harin da Isra'ila ta kai a lokacin da suke jiran karbar agaji. An kuma ruwaito cewa, gawawarwakin mutane a kan hanyoyi arewa maso yammacin Gaza.
Karin bayani:Isra'ila ta kashe sama da mutum 400 a harin Gaza
A cewar shaidun gani da ido, mutanen sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke jiran motacin agaji a kusa da wata iyaka da Isra'ila. Gidauniyar bayar da agaji ta Gaza (GHF), da ke samun goyon bayan Isra'ila da Amurka ce ke raba agaji a arewacin Rafah, sai dai har yanzu gidauniyar bata ce uffan ba a kan lamarin. Alkalumman Majalisar Dinkin Duniya sun yi nuni da cewa, kimanin mazauna Gaza miliyan biyu ne suka dogara kacokan kan tallafi.