Gobarar tankar man fetir ta kashe mutane 55 a Nijar
May 6, 2019Talla
Mutanen sun mutu ne a daran Lahadi zuwa Litinin a lokacin da suke kokarin dibar man fetir a wata tankar da ta fadi, fitar birnin Yamai kan hanyar zuwa Dosso kafin daga bisanin ta yi bindiga ta kama da wuta. Wakilin DW a birinin Yamai ya ce yawancin wadanda suka mutun sun kone kurmuse yayin da wasu 36 suke cikin wani mawuyacin hali.